Ƙura Takai Bango ! Budurwa ƴar Arewa ta roƙi mahaifin ta yayi mata aure, ko na dole ne
Wata matashiyar budurwa mai suna Hafsat Samaila tare da shafin Twitter @Oummieeh ta koka a kan gajiya da zaman kadaici babu aure.
Matashiyar wacce ta fito daga yankin arewacin kasar ta roki mabiya shafin sadarwa ta Twitter a kan su taya ta rokon mahaifinta kan yayi mata aure domin a cewarta a yanzu babu abunda take so sama da hakan.
Kamar yadda Legit na ruwaito,Hafsat ta kuma jaddada cewa a shirye take tayi zaman aure koda kuma na dole za a yi mata.
Ta wallafa a shafin nata: “Ya ku Ayyuhan nas..dan zaman arxiki da muke a tuwita.. Ku cewa baba na aure nake so..ko na dole ne zan zauna.”
??Ya ku Ayyuhan nas..dan zaman arxiki da muke a tuwita.. Ku cewa baba na aure nake so..ko na dole ne zan zauna??????????
— Hafsat Samaila mabai (@Oummieeh) December 5, 2020
Tuni dai jama’a suka yi tururuwan zuwa bangaren yin sharhi a karkashin rubutunta don bayyana ra’ayinsu.
@KabirMtz ya wallafa:
“Toh, tunda kin shirya zanzo na biya sadakin aurenki gobe…Indai zaki zauna da kishiya babu matsala to zanzo gaisuwa gobe..”
@y_saneey ya ce:
“Hhhhhhhhh plx duk wacce xaa yiwa mawa auren dole sae ta nemo nii.”
@Usman_M_Isah ya ce:
“@sameenuabdoul @AlieAbba kune makwafta sai ku taimaka ku isar da Saqo.”
@FalakinKano ya ce:
“In Shaa Allah, zan kira shi a kan haka. Kina ruwa……”
ranka shi dade sir, idan na yarda nayi tsaurin ido, za’ace nayi rashin kunya??
— Hafsat Samaila mabai (@Oummieeh) December 5, 2020
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






