Minista Sheikh Pantami Ya Fi Kowanne Minista Kokari A Nijeriya”
Jaridar Premium Times ta ayyana Ministan Sadarwa Sheikh Isa Ali Pantami a matsayin Ministan da yafi kokari cikin ministocin kasar nan baki daya, duba da yadda Ministan ya maida hankali wajan kawo cigaba a ma’aikatun da yake shugaban ta.
Minista Sheikh Pantami ya yi matukar kokari a wajan farfado da tattalin arzkin kasarmu ta hanyar kawo tsare tsare na cigaba a hanyoyin sadarwar zamani, musamman ma a wannan lokaci da tattalin arzkin kasashen duniya ya karye saboda cutar Coronavirus da tayi silar karyewar dukkanin tattalin arzkin kasashen mu.
Minista Sheikh Pantami ya kawo sabbin cigaba ta bangare daban daban da suka shafi sabbin fasahar sadarwar zamani, koyar da sana’o’in zamani ga al’ummar Nigeria, takawa layukan sadarwa burki wajan kwashe dukiyoyin al’umma, a lokutan kiran waya da amfani da DATA, ya takawa Hukumomi da yawa burgi don ganin sun yiwa ‘yan Nigeria adalci a cikin ayyukan su, ya tilasta duk wani dan Nigeria yin registan layukan sadarwar da mutum ya mallaka.
Haka zalika Minista Sheikh Pantami ya gina manya manyan sabbin cibiyoyin sadarwar zamani a dukkanin Jihohin Nigeria da ba zasu kirgu ba, ya samawa ‘yayan talakawa aiki da ba zasu kirgu ba, ya tallafawa al’umma daban daban da babu wanda zai iya kiyasta a dadinsu sai dai Ubangiji, ya kawo cigaba daban daban da Ba’a taba samun wani Minista a Nigeria da yayi makamancin aikin da yayi ba.
Duba da irin wannan kokarin na Ministan Sadarwa Sheikh Isa Ali Pantami da yake yi, Jaridar Premium Times ta ayyana shi a matsayin gwarzon ministan da babu kamarshi kaff a Nigeria, babu wanda yayi makamancin aikin da yayi duk a cikin ministocin kasar nan.
Da Wannan muke kira ga Ministan Sadarwa Sheikh Isa Ali Pantami, da ya kara dagewa Ubangiji kan ni’imar da ya bashi, ya kara dagewa ya cigaba da gudanar da ayyukan shi kamar yadda yake yi, Ubangiji yana tare dashi kuma zaici gaba da taimakonsa.
Marubucin rariya Comr Abba Sani Pantami ne ya wallafa a shafinsu