Labarai

Allah Bai Manta Dani Ba: Bidiyon Budurwa Mai Shekaru 52 da Tayi Auren Farko

Bayan kwashe tsawon shekaru tana jira, wata mata ‘yar Najeriya mai shekaru 52 ta hadu da abokin rayuwarta kuma sun shige daga ciki.

Wata mai amfani da shafin TikTok mai suna Ogechi Gideon Udofia ta wallafa bidiyon wata mata cikin rigar bikinta a ranar aurenta tare da shawartar masu amfani da yanar gizo da cewa lokacin Ubangiji shi ne daidai. Jaridar Legit na ruwaito

Ta ce burinta ya cika

A wani bidiyo, an ga amaryar na bayyana yadda take ji a kan yadda daga karshe tayi aure.

Matar mai cike da farinciki ta ce ji take kamar ta ruga da gudu, tare da zaro idanuwanta gami da cewa Ubangiji ya yi nasa ikon.

A cewarta:

Yau rana ta ce. Ina matukar murna. Buri na ya cika. Ji nake kamar in ruga da gudu. Ubangiji ya yi nasa ikon. Ina cikin farin ciki.”

Jama’a sun yi mata addu’o’i
Babu jimawa jama’a suka yi caa inda suka dinga kwarara mata addu’o’in fatan alheri.

Flora Abraham675 ta ce:

Kai gaskiya ina taya ki murna, Ubangiji zai baka mamaki ta yadda ba za ka iya misalta farincikin da za ka shiga ba. Nan da watanni 9 za mu taya ki murna saboda babu abun da ya gagari Ubangiji.”

Queen Amina ta ce:

Ina taya ki murna, ina fatan za ki samu cikakken farin ciki da fatan gidanki zai zama cikin wadanda suka fi kowa farinciki Amin.”

richloretta ta ce:

Kai wannan wata kalmace da na gani a cocina, gaskiya kin yi matukar kyau.”

Angel ta ce:

Gaskiya ina taya ki murna, Na shafi tabaraki daga muwafakar da Ubangiji ya miki, na yarda Ubangiji ne ke da lokaci, Ubangiji ya albarkaci wannan auren naku.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button