Kannywood

Bidiyo: Allah Sarki ! Mama Daso Ta Fashe Da Kuka Ganin Yadda Ofis Din Mansurah Isah Ya Koma

Saratu Gidado Wato Mama Daso takai ziyarar jaje a ofishin Mansura Isah wanda yan bata gari suka lalata a birnin Kano.
Ofishin na Mansura dai wanda wasu bata gari ne suka fasashi inda suka kwashe dukkanin abinda ke cikinsa wanda hakan ya jawo babbar asara ga ita Mansura Isah.
Mansurah Isah ta kasance shugabar gidauniyar tallafawa al’umma musamman wadanda basu da hali a yayin wata matsala kamar ta rashin lafiya, bukatar abinci, muhalli, hidimar marayu ko marasa galihu da sauran makamantasu.
An kaima wannan ofishi dai nata hari ne a yayin zanga-zangar nan ta endsars wacce ta janyo mummunar asara ta dukiya da kuma rayuwa a sassa daban-daban na Nigeria.
A cikin wannan bidiyo Mama Daso ta fashe da kuka ganin halin da ofis din ya koma da kuma duba da irin mummunar asarar dukiya da akai.
Ga dai wannan bidiyon a kasa:
https://youtu.be/PjaGiv69B4Y

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button