Labarai

ABUN ƁOYE YA FITO FILI: Dalilin da ya hana Mamman Daura halartar shagalin bikin Hanan Buhari

Advertisment

Duk da bayyana Mamman Daura da aka yi a matsayin uban taron auren Hanan Buhari da Muhammad Turad, ɗan uwan shugaban ƙasar kuma shaƙiƙinsa bai samu halartar taron bikin ba.

Jaridar Sahara Reporters ta wallafa cewa, rashin halartar Mamman Dauran ba ya rasa alaƙa da tafiyar da yayi zuwa Dubai domin a duba lafiyar sa ba sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.

Idan za mu tuna, Mamman Daura ya yi tafiya zuwa Ingila tun a cikin watan Augustan da ta gabata, An fara raɗe-raɗin rashin lafiyar sa amma wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya ƙaryata hakan, A bidiyon an ga Mamman Daura na waya da shugaba Buhari a yayin da yake hutawar sa a wani masauki da ke Ingila.

Tsohon ɗan jaridar na daga cikin waɗanda ake zargi na da kusanci da shugaban ƙasa Buhari kuma suna amfani da hakan wurin juya akalar mulkin ƙasar nan, Tuni dai an gano cewa Mamman Daura na da ciwon ƙoda, wanda hakan yasa yake ziyartar ƙasahen Turai domin duba lafiyar sa.

Advertisment

Lagit.Hausa ta ce wata majiya wacce ta tabbatar da rashin halartarsa bikin, ta ce an yi shagalin bikin a babban ɗakin taron da ke kallon ofishin shugaban ƙasa, a maimakon ɗakin taro na banquet inda aka saba saukar manyan sha’anoni.

Majiyar ta sake jaddada cewa, mutum 80 kacal suka halarci taron bikin saboda jaddada kiyaye dokokin daƙile yaɗuwar muguwar cutar korona, Har yanzu kuwa rashin halartar Daura bikin ya janyo cece-kuce a tsakanin ƴan siyasa, ballantana makusantan shugaba Buhari.

A wani labari na daban, bidiyon yadda ake ruwan kuɗi a bikin ɗiyar shugaban ƙasar Najeriya, Hanan Buhari da Turad Sha’aban shima ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani.

Wannan bidiyon ya bayyana ne bayan a kalla watanni biyu da bidiyon ɗan antoni janar kuma ministan shari’a, Abdulazeez Malami, ya bayyana inda ya yi aure kuma aka dinga watsi da Naira a jihar Kebbi, A bidiyon an ga angon da amarya tare da jama’a da yawa sun watsa musu kuɗi. Duk da ba sabon abu bane watsi da  kuɗi a biki, babban bankin Najeriya ya hana wannan lamari a sashi na 21 na dokokinsa na 2007.

Hakan zai iya sa a ci tarar mutum N50,000 ko ɗaurin watanni shida a gidan maza a saboda wannan dokar ta babban bankin Najeriya, ƴan sanda sun saba kama jama’a da ke siyar da sabbin kuɗaɗe a wuraren bukukuwa. Sannan a gefe guda haka yana har zuƙa al’umma Najeriya musamman yadda ake wani irin yanayi na ƙuncin rayuwa da tsadar abinci a birni da ƙauyuka.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button