Uncategorized
Aisha ta ce mai zanen barkwanci Bulama bai yi wa bikin ƴarta adalci ba
Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta ce zanen barkwancin da Mustapha Bulama ya yi da ke nuna yadda take nuna wa ƴan Najeriya hotunan bikin yarta Hanan Buhari su kuma yan ƙasa na nutsewa a cikin kogi saboda wahala ‘”babu adalci a ciki”.
Mai magana da yawun Aisha, Aliyu Abdullahi ya shaida wa BBC cewa ƴaƴan kowanne shugaba na da damar aure idan lokaci ya zo ko da ƴan kasa na jin daɗin mulkinsu ko akasin haka.
“Zanen barkwancin Mustapha Bulama da ke yawo babu adalci a ciki saboda bikin ba shi da wata alaƙa da yanayin da yan kasa suka tsinci kansu, kuma saboda irin haka ne ya sa wata guda kafin bikin, shugabar tawa ta tattauna da ma’aikatanta cewa ba ta son a yayata bikin saboda za a taƙaita hidima.”
“Hoton da shugaba ta (Aisha Buhari) ta wallafa na ma’auratan a soshiyal midiya na bayan biki ne domin ta gode wa wadanda suka aike da fatan alheri da kuma sanar da ƴan kasa.
”Ina iya tabbatar muku cewa bikin Hanan Buhari shi ne wanda kwata-kwata babu armashi kuma aka taƙaita idan aka kwatanta da bukukuwan baya da aka yi a kasar nan.”
Bbchausa na ruwaito,Kakakin nata ya kuma ce bidiyon da aka rinka yaɗawa da ke nuna yadda mutane ke yi wa ma’auratan liƙi ɓangaren dangin ango ne bayan an kai musu amarya.
“Wannan bidiyon da ke nuna mutane na liƙi da kudin naira ba a Abuja ba ne a gidan surukan Amarya ne bayan ta isa gidan dangin mijin a Kaduna,” a cewar kakakin uwargidan Buhari.
Aliyu ya kuma ce uwargidan shugaban kasa ta damu da annobar cutar korona da dokokin da likitoci suka gindaya da masana kimiyya, kuma ta tabbatar da hidimar da ta shirya mutane sun bi waɗannan dokoki.
”Da an ɗaga bikin”
A ranar 4 ga watan Satumban 2020 aka ɗaura auren Hanan Buhari a lokacin da ƴan Najeriya da dama ke ƙorafin mawuyancin halin da suke ciki saboda hauhawar firashin kayan abinci da man fetur da wutar lantarki.
Wani Sani Musa da ke yawan tsokaci a shafukan sada zumunta mazaunin Kano a arewacin Najeriya ya shaida wa BBC cewa abin da ya kamata iyalan shugaban kasa su yi shi ne ɗage bikin zuwa lokacin da lamura za su daidata a ƙasar.
“A ganina, ina ganin bai kamata a yi wannan bikin ba a yanzu, saboda ƙasar na cikin yanayi na korafi saboda wahalhalun da ake ciki.
”Ga ɗan Najeriya da ke neman abin kai wa baki sannan babu kuɗin biyan wuta ko ruwa, sannan ya yi kiciɓus da hotunan auren ɗiyar shugaban kasa da bidiyo na yawo dole ya fusata,” a cewarsa.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com