Labarai
MATSALAR TSARO: Masu Zanga-zanga A Jihar Katsina Sun Nemi Buhari Ya Yi Murabus (A Cikin Hotuna)
Daga Indabawa Aliyu Imam
Matasa a kauyen Turare dake karamar hukumar Dutsin-Ma a jahar Katsina sun fito zanga-zangar neman Buhari ya sauka daga mulki, saboda hare-hare da ‘yan bindiga ke yawan kai musu.
Mazauna yankin dai sun fito ne sakamakon wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai musu, wanda ya janyo asarar rayuka da dama, jama’a masu yawa suka rasa muhallinsu yayin da aka yi wa mata da yawa fyade.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com