Labarai
Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Rajiun! Allah yayiwa AbdulMalik, ‘dan Shaykh Ja’afar Mahmud Adam (RH) Rasuwa
Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Rajiun! Allah yayiwa AbdulMalik, ‘dan Shaykh Ja’afar Mahmud Adam (RH)
Majiyarmu ta samu wannan labari ne daga shafin Sheikh Dr Ali Isah Pantami
Yana mai cewa
“Na samu labarin rasuwar AbdulMalik, ‘dan Shaykh Ja’afar Mahmud Adam (RH).
Ina mika ta’aziyya zuwa ga yan’uwansa da iyayensa, kan Allah Ya jikansa, Ya jikan iyayenmu da sauran yan’uwanmu, kuma Ya kyautata namu bayan na su,…
“Wanda ya mutu, bai yi sauri ba. Mu da muke nan bamu dade ba, sai mun zo”… in sha Allah”
Majiyarmu ta samu daga wata majiya cewa Abdulmalik ya rasu ne ta sanadiyyar hadarin mota a hanyar Katsina.
A madadin mabiyan shafin Hausaloaded da mai Hausaloaded na miki Ta’aziyyar rasuwar abdulmalik Allah ya jikansa yayi masa rahama amen.