Labarai
Sanarwa Ga Matsan Da Suke Neman Shiga Aikin ‘Dan Sanda
Advertisment
Rundinar ‘yan sandan Nigeria tana sanar da matasan da suka cika online form na neman shiga aikin ‘dan sanda cewa za’a fara tantancesu nan da kwana hudu masu zuwa, wato ranar Litinin 24-8-2020, za’a kammala tantancewar zuwa ranar 6-9-2020
Za’ayi tantancewar ne a kowace jiha da birnin tarayya Abuja, ana bukatar matasan da su je gurin tantancewar da wadannan abubuwa kamar haka:
1- Lambar shaidar katin ‘dan kasa, National Identity Number (NIN).
2- Takardu original da kwafi na kammala karatun sakandare, shaifar katin haihuwa, shaidan indijin, file guda biyu, hoto passport, sannan a saka fararen kaya da farin gajeran wando.
3- Ayi printing takardan da aka cika online form aje gurin tantancewar dashi
4- Sai kuma takardan garanto.
4- Sai kuma takardan garanto.
Wanda bai samu damar zuwa gurin tantancewar da Datti Assalafy ya ruwaito,wadannan abubuwa hudu da ake bukata ba, to ba za’a kulashi ba, kuma za’a gudanar da tantancewar bisa kiyaye dokokin yaduwar cutar Coronavirus.
Maigirma shugaban rundinar ‘yan sandan Nigeria IGP Muhammad Abubakar Adamu yana mai tabbatar da cewa diban sabbin ‘yan sanda dubu 10 kyauta ne, yana gargadin wadanda suke neman aikin da kar su kuskura su bayar da kudi wa ‘yan damfara, ya bayar da umarni a kama ‘yan damfara, kuma yace zai tabbatar da adalci wajen diban ‘yan sandan
Sanarwa daga kakakin rundinar ‘yan sanda na kasa DCP Frank Mba
Allah Ya bawa mai rabo sa’a
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com




