Labarai

Yadda ’yan Najeriya su ka kasa gode wa Buhari ne ya fi ci min tuwo a kwarya – Lai Mohammed

Ministan Yada Labarai da Inganta Al’adu Lai Mohammed, ya bayyana cewa a matsayin sa na minista,babu abin da ke bata masa rai irin yadda ’yan Najeriya su ka kasa gode wa dukkan kokarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi, duk kuwa da cewa babu wadatattun kudi a hannun gwamnati.
Lai ya yi wannan bayani a cikin wani shiri na Musamman da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).
Kamar yadda premium times na ruwaito ya kara da cewa duk kuwa da matsanancin karancin kudade da gwamnatin nan ke fama, a haka din ma a tarihin Najeriya babu wata gwamnati da ta taba bijiro da ayyukan inganta rayuwar talata na kawar da talauci, inganta rayuwar marasa galihu da matan karkara da kuma samar da ayyukan yi ga matasa, kamar gwamnatin Buhari.
Ya ce abin da kawai ya ke jin haushi shi ne yadda wasu ‘yan Najeriya sun kasa yin hamdala da godewa ga gwamnatin Buhari kan kokarin da ya ke yi, sai kawai wuraren da gwamnatin ta samu cikas su ke ta yayatawa.
Daga nan Lai ya shiga tuna wa ‘yan Najeriya irin yadda gwamnatin da su ka gada ta tara makudan kudade daga ribar danyen man fetur, wanda a yanzu kuwa farashin sa ya fadi kasa warwas sakamakon barkewar cutar korona a fadin duniya tsawon shekara daya cur.
“Amma mu a lokacin da annobar korana ta barke bagatatan a duniya, aka kulle kasashe, sai ta ta kai babu kasar da ke bukatar danyen mai a duniya. Aka bar mu da biyan ladar ajiya a inda mu ke tara danyen mai din, domin babu mai bukata kwata-kwata.
“Duk da faduwar farashin danyen man fetur da gagarimar matsalar tsaro, har yau wannan gwamnti ba ta rage ma’aikata ba, ba ta kuma kori ma’aikaci ko da ya ba da nufin rage wa gwamnati radadin matsin tattalin arziki sakamakon barkewar korona.” Inji Lai.
Lai ya nuna rashin jin dadin yadda ‘yan Najeriya ba su godewa da irin kokarin da wannan gwamnati ta yi domin bunkasa rayuwar marasa galihu da su ka hada da tallafin korona, lamuni ga manoma da kananan masu sana’o’i, Tradermomi, N-Power da sauran ayyukan jinkai, agaji da bunkasa rayuwar marasa galihu da ake gudanarwa a karkashinn wannan gwamnati.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button