Labarai

Morsi ya yi shahada – Shugaba Erdogan

Kungiyar Muslim Brotherhood ta yi ikirarin cewa an hana marigayi Mohammed Morsi samun kulawar lafiya kuma an tsare shi cikin kadaici tsawon shekara shida a gidan yari.

Tsohon shugaban mai shekara 67 ya yanke jiki ya fadi lokacin sauraron bahasinsa kan zarge-zargen leken asiri a kotun birnin Alkahira.

Muslim Brotherhood ta zargi hukumomin Masar da alhaki kan mutuwarsa, yayin da Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana Mursi a matsayin shahidi.

“Ganin yadda marigayin, wadda aka yi wa shari’ah a kotun juyin mulki kuma aka yanke masa hukuncin kisa, ya ja numfashinsa na karshe a kotu, hakan wata manuniya ce ta gallazawar da aka yi masa tsawon shekaru, shi da jama’arsa.

Erdogan ya ce zai riki shugabancin kasar Masar na Abdel Fateh al-Sisi da alhaki kuma tarihi ba zai taba mantawa da ‘yan kama-karyan da suka yi sanadin mutuwar Morsi ba.

Shi ma wani dan majalisar dokokin Burtaniya na jam’iyyar Conservative, Crispin Blunt, wanda ke daya daga cikin mutanen da suka yi ta bayyana damuwa bara game da yadda ake tsare da shugaban, ya bukaci gudanar da bincike na kasashen duniya.

Ya fada wa BBC cewa halin da aka tsare Morsi ya yi muni matuka, kuma sun fada a lokacin, cewa idan ba a kula da lafiyarsa cikin gaggawa ba, hakan zai yi lahanin dindindin ga lafiyarsa, ko ma ya zama sanadin cikawarsa.

“Kuma ga shi yanzu abin da muka fada ya tabbata, don haka sai gudanar da bincike mai zaman kansa, don tantance musabbabin rasuwarsa” in ji Crispin.

Daya daga cikin masu adawa da Morsi, Khaled Dawoud na jam’iyyar National Salvation Front, ya ce ba a yi wa marigayin adalci.

A cewarsa su jam’iyya ce da ta rika kiran a mutunta doka, a mutunta hakkin dan Adam kuma ya ce ya yi imani an hanawa Morsi wasu daga cikin hakkokinsa na bil’adama ciki har da ‘yancinsa na samun kula da lafiya.

Ma’aikatar cikin gidan Masar dai ta sanya kasar cikin ta-kwana.

Rasuwar Mohammed Morsi ta zo ne ‘yan kwanaki gabanin fara gasar cin kofin Afirka da Masar ke karbar bakunci.

® Bbchausa

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button