Labarai

RASHIN UWA: Kishiyoyin Mahaifiyarsa Sun Daure Shi A Tirken Awaki Na Tsawon Shekaru Biyu



Kamar yadda labari yazo mana wannan yaron da kuke gani sunan sa Jibril Aliyu kuma yana Unguwar Badariya Area dake cikin garin Birnin Kebbi, a jihar Kebbi.

Labari ya same mu cewar kishiyoyin mahaifiyar sa ne suka daure shi cikin turken tumakai na tsawon shekaru biyu tun bayan rasuwar mahaifiyarsa.

Kuma bai samu kulawa na ba shi abincin ci, saidai ya ci abincin dabbobi, inda yanzu haka jami’an tsaro suka kama kishiyoyin mahaifiyar shi da suka daure hadi da mahaifinshi inda suka garzaya da su zuwa ofishin ‘yan sanda.

Kuma  bayanai sun tabbatar da cewar an garzaya da yaron zuwa Asibitin Sir Yahaya dake Birnin Kebbi don ba shi agajin gaggawa.

Allah ya ba shi lafiya, kuma ya shirya mata masu irin wannan hal.i Amin.

Daga Real sani Twoeffect Yawuri a shafin Rariya

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button