Masha Allah ‘Manaraabp’ daga kungiyar IZALA yake, kowa zai iya cikawa karanta yadda ake cikawa Tare Link
Daga Ibrahim Baba Suleiman
Website na Manaraabp gaskiyane, kuma kungiyar IZALA ce ta umurci kamfanin Manara da ta jagoranci wannan tsari na karbar bashi marar kudin ruwa da su malaman suka yi ta kai ruwa rana akan samuwar sa, domin musulman kasar su amfana da bashin.
Dan haka duk wani musulmi zai iya cikawa, ‘Website din www.manaraabp.com‘ site din daga garemu yake, duk Wanda ya ganshi ya cika, kuma ya sanar da ‘yan uwa su cika. Nan gaba kadan za’a kira taron tantancewa a jihar da mutun yake.
Kamfanin Manara shi ya dauki nauyin wayar da kan mutane, tare da jagorantarsu har akai ga gaci. Ba’a karban ko kwabo wajen cikawa, kuma babu tsarin karban kudi a wajen masu cikawa, a kiyaye wannan.
Wannan App da ake cikawa, ana neman bayanan sirrinka ne, Wanda aka bashi cikekken tsaro domin masu kutse. Bayan kamalla karbar bayananka, duk sanda za’a baka bayanai za’a tura maka ta e-mail dinka da wayar hannunka.
Allah ya mana jagora. Amin
Jibwis Nigeria

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





