Labarai

ZANCEN GASKIYA: Kungiyar Izala Ba Ta Ce Zata Hada Kai Da Bankin CBN Domin Bada Rancen Kudi Ba

Advertisment

Daga Ibrahim Baba Suleiman shine director general na social media na Kungiyar Izala ta kasa.

Shugaban Kungiyar wa’azin musulunci ta IZALA Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, yace kungiyar IZALA bata ce zata hada kai da babban bankin kasa (CBN) dan ta rabawa mutane rancen kudin noma ba.
Sai dai kungiyar tace CBN ta fitar da ka’idojin da za’a bada rance Wanda babu kudin ruwa a cikin sa.

Kungiyar  IZALA ta dade tana jiran wannan rana, da za’a samarwa mutane bashi daga CBN Wanda babu ruwa a cikinsa, kungiyar tayi ta Kokari wajen samar da wannan  tsari daga CBN Wanda a karshe Allah yasa aka dace.

Wadanda suka sani sun sani, Babu yadda za’ayi bankin CBN yayi harka da wata kungiya kai tsaye a maganar bashi, sai dai tayi harka da bankuna wadanda ake kira (FINANCIAL INSTUTION) Irinsu Ja’iz Bank, Starling Bank, da Taj bank. To wadannan bankuna ta hannunsu CBN zata raba wadannan kudade.

Ka’idojin da CBN ta fitar mafiya yawa basu San da su ba, shine kungiyar JIBWIS ta umurci kamfanin Manara da su jagoranci wayar da kan mutane har akai ga gaci, musamman shugabannin IZALA na jihohin kasar, akan wannan rance da CBN zata bada. za’a bada.

Sheikh Lau yace babu inda akace kungiyar IZALA zata hada kai da Dr. Bashir Umar Ali dan ta rabawa mutane wannan kudi ba, ita dai JIBWIS tana da masaniyar yadda za’a bada kudaden, ba tare da kowa ya kashe sisin kwabo ba Wanda babu gaira babu dalili.

A karshe shugaban yace babu inda kungiyar ta taba ambatar sunan Dr. Bashir Umar Ali akan wannan harka na Manara App ba, JIBWIS na da alaka da kyakkyawar fahimta tsakanin ta da Dr. Bashir,  duk kuwa da JIBWIS ta San muhimmancin sa, da kwarewar sa a wannan tsari da CBN ta fitar, Kuma abun da Dr. Bashir ya wallafa a shafinsa na Facebook gaskiya ne, domin babu inda muka taba tuntubarsa akan wannan harka, wasu ne kawai suka tsara labarin karya suka yada.

Sheikh Bala Lau yace kungiyar zata ci gaba da binciko irin wadannan tsari ita kuma zata ci gaba da wayar da kan al’umma domin ayi da su.

A karshe shugaba Bala Lau yayi kira ga masu irin wadannan dabi’a ta kirkirar Labarin karya suna yadawa mutane da suji tsoron Allah, dan wata rana za’a hadu da shi.

Jibwis Nigeria

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button