NAHCON ta baiwa Hajara Dan Azumi wadda ta lashe gasar musabaƙa kujerar hajji


Hukumar kula da alhazzai ta Nijeriya ta karama hafiza Hajara Ibrahim dan azumi da kujerar hajji akan jajircewa da tayi akan lashe gwarzuwar musabaƙa da ankayi a kasar jordan a watan da ya gabata.
Hajiya Fatima Sanda Usara mataimaki ta musamman akan hukumar alhazzai ta Nijeriya ce ta fitar da wannan sanarwa a ranar juma’a.
Hajiya fatima ta kara da cewa shugaban hukumar alhazzai Malam Jalal Ahmad Arabi ya taya hafiza hajara dan azumi da murna lashe ta ɗaya a gasar musabaƙa ta mata da ankayi ta duniya.
Anyi gasar musabaƙa ne a watan fabrairu 17 ga wata zuwa 22 ga wata, wanda akeyi duk shekara karkashin kulawar hukumar kula da ma’aikatar lamuran addinin musulunci da zama lafiya a kasar jordan.
Hafiza dan azumi yar shekara 19 wace take dalibar makarantar islamiyyar Abubakar saddiq community Gombe, hajara yanzu tana karatu a jami’ar gombe aji biyu 200L inda take karatun sashen botony, Dan azumi ta wakilci najeriya wajen musabaƙa Alkur’ani ta hizab 60 da tajwid, ta samu maki 99.5% a cikin kasashen 39 da sunka halarci musabaƙa, wannan makin da ta samu ya bada nasarar lashe lamba ta daya a gasar.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






