Labarai

Za a haifi jarirai akalla 365,595 a Jihar Jigawa a wannan shekara ta 2023

Gwamnatin Jigawa ta bayyana cewa a cikin wannan shekara ta 2023 za a haifi jarirai akalla 365,595 a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar Abdullahi Kainuwa ya sanar da haka a taron inganta amfani da dabarun bada tazarar haihuwa da aka yi a garin Dutse ranar Alhamis din makon jiya Majiyarmu ta samu ta majiyar premium Times Hausa.

A jawabin da ya yi a taron Kainiwa ya ce mata na samun dabarun bada tazarar haihuwa a asibitocin jihar.

Ya ce daga cikin jarirai 365,595 din da ake sa ran za a haifa a jihar an haifi jarirai 273,000 zuwa watan watan Yulin 2023.

Za a haifi jarirai akalla 365,595 a Jihar Jigawa a wannan shekara ta 2023
Za a haifi jarirai akalla 365,595 a Jihar Jigawa a wannan shekara ta 2023 Hoto/Facebook

“Saura jarirai 1,000 ake sa ran za a haifa zuwa karshen shekara.

Kainuwa ya ce a jihar akwai mata 1,608,616 dake haihuwa sannan gwamnati na da burin ganin cewa nan da shekara ta 2027 mata kashi 30% daga cikinsu na samun dabarun bada tazarar haihuwa a jihar.

Bisa ga alkalaluman da gwamnati ta samu daga yawan matan dake zuwa asibiti awon ciki da haihuwa ya nuna cewa mata da dama basu zuwa asibiti.

A jihar an samu karuwar kashi 18.2% a 2023 daga kashi 6.8% da ake da shi a 2015.

Bisa ga bin diddigin bayanan kasafin kudin jihar, PREMIUM TIMES ta cewa gwamnati bata ware isassun kuɗaɗe wa fannin bada tazaranr haihuwa tun daga shekarun 2020 zuwa 2023.

A kasafin kudin shekara na jihar gwamnati ta ware wa fannin naira miliyan 10 a 2020 amma babu kudin da fannin ta samu har shekarar ta kare.

A shekaran 2021 gwamnati ta ware wa fannin naira miliyan 20 inda naira miliyan N7,628,000 ne kawai fannin ta samu shima din a kurarren lokaci.

A shekarar 2022 gwamnati ta ware naira miliyan 30 amma naira miliyan 23 fannin ta iya samu a wannan shekara.

A shekaran 2023 gwamnati ta ware naira miliyan 35 amma zuwa yanzu babu ko sisi da ya shiga asusun fannin bada tazarar haihuwa.

A bayanin da ya yi Kainuwa ya ce ya zama kwamishinan kiwon lafiyar jihar wata daya da ya gabata amma ya tabbatar cewa zai yi kokari wajen ganin fannin ta samu kaso mai tsoka daga kasafin kudin jihar nan gaba

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button