Labarai

Gwamna Zulum Ya Tona Asirin Wandana Suke Cin Amana A Yaki Da Ta’addancin Boko Haram

Advertisment

Wannan jawabi na tonon asiri  BBC Hausa suka ruwaito cewa Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum yace jami’an tsaro na yin zagon ƙasa a yunƙurin kawar da ƙungiyar Boko Haram

Wato turace ta kai bango, Gwamna Zulum yace bai zai iya yin shiru ba ana ci gaba da kashe al’ummarsa da sunan ta’addancin Boko Haram saboda rantsuwar da yayi da Al-Qur’ani tsakaninsa da Allah cewa zai kare rayuka da dukiyoyin jama’ar Borno

Khadimul Ummah ya yi wannan jawabin ne a lokacin da wasu gwamnonin Arewa suka kai masa ziyaran jaje bayan harin kwanton bauna da ‘yan Boko Haram ko wasu maciya amanar tsaron Nigeria suka kaddamar masa a garin Baga da nufin hallakashi

Advertisment

Farfesa Babagana  Umara  Zulum yace akwai bukatar Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya san cewa cin amana da zagon kasar da ake yi a yaki da ta’addancin Boko Haram shine ya kawo cikas wajen kawo karshen ta’addancin Boko Haram daga doron duniya

Gwamnan yaci gaba da cewa: “ba na neman wa’adi na biyu, idan Allah Ya nufe ni da kammala wannan wa’adi na farko to Alhamdulillah, amma ni a matsayina na gwamna, na yi shiru al’umma jihar Borno miliyan shida su mutu, su ƙare, hakan ba zai zama alheri gare ni ba, nayi rantsuwa tsakanina da Allah zan kasance mai gaskiya ga al’ummata,” in ji Gwamna Zulum

Gwamna Zulum ya kuma tuhumi abin da ya sa sojojin Nigeria suka hana dubban mutanen da rikicin Boko  Haram ya raba da gidajensu komawa garuruwa da gidajensu, saboda su sojojin ne  ke noma a filayen mutanen, shiyasa basa son mutanen su koma

BBC ta tuntuɓi rundunar sojin Nigeria don jin martaninta game da waɗannan manyan zarge-zarge, amma rundinar sojin ta ce ba ta sa-in-sa da shugabannin siyasa, sojoji ba za su ce uffan kan zarge-zargen Gwamna Zulum ba, saboda su ba sa musayar yawu da shugabannin siyasa

Nigeria kenan!, dadin abin wa’adin mulki zai kare watarana, kuma akwai ritaya, sannan akwai tsufa, sihiri/tsafi shima yana karyewa, sannan uwa uba akwai mutuwa, dolen uban mutum ya mutu watan watarana

Yaa Allah Ka kare Gwamna Zulum
Yaa Allah Ka tona asirin maciya amanar tsaron Nigeria
Yaa Allah Ka karemu daga sharrinsu

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button