Labarai

Jami’an tsaron Nijar sun cafke kasurgumin dan bindiga Baleri da hukumomin Nijeriya ke nema

Advertisment

Jami’an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun sanar cewa cmsun yi nasarar kama kasurgumin dan ta’addar nan mai suna Baleri da hukumomin Nijeriya suka sanar cewa su na nemansa ruwa jallo.

Jami’an tsaro na rundunar nan ta musamman masu lakabin ‘farautar bushiya’ ne dai dake aikin kawo tsaro a jihar Maradi suka yi nasarar kama wannan dan bindiga dan asalin karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara, majiyarmu ta samu labari daga Dclhausa.

Dan bindigar da ke gudanar da ayyukan sa a tsakanin kasashen na Nijar da Najeriya sojojin sun ce sun yi nasarar cabke shi ne a karamar hukumar Guidan Roumdji ta jihar Maradi a lokacin da yake tsaka da tsare-tsaren yadda za su kai hare-hare a kasashen biyu da yaran sa.

Jami'an tsaron Nijar sun cafke kasurgumin dan bindiga Baleri da hukumomin Nijeriya ke nema Jami'an tsaron Nijar sun cafke kasurgumin dan bindiga Baleri da hukumomin Nijeriya ke nema

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button