Labarai
Da mun so Da mun yi amfani da jami’an tsaro wajen Murkushe ‘yan Adawa~ Shugaba Buhari
Advertisment
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa da sun so da sun yi amfani da jami’an tsaro a jihohin da suka fadi zabe sun murkushe ‘yan Adawa.
Saidai yace saboda bin doka da kuma kasar ce a gabansu shiyasa ba su yi hakan ba.
Shugaban ya bayyana hakane a lokacin ganawar da yayi da gwamnonin Arewa Maso gabas,kamar yanda Hutudole ya fahimta a jiya a fadarsa. Ganawar ta kuma samu halartar shuwagabannin tsaro.
A ganawar shugaban ya bayyana cewa sun samu matsalar kudi/da kayan aiki, kamar yanda hutudole ya fahimta hakanan kuma yace annobar cutar Coronavirus/COVID-19 ta kawo musu cikas wajan cimma manufofin gwamnatinsu.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)



