Labarai
An saka dokar ta-ɓaci a Beirut bayan fashewar da ta kashe mutum aƙalla 113
Advertisment
Ga abubuwan da muka sani game da fashewar sinadarai a Beirut na Lebanon ranar Talata zuwa yanzu:
- Ministan yaɗa labarai ya sanar da saka dokar ta-ɓaci ta tsawon mako biyu
Majalisar ministoci ta nemi jami’an tsaro da su tabbata ba su bari wani ya je wurin da fashewar ta faru ba a ranar Talata
- Fiye da mutum 100 ne ba a san inda suke ba kuma ana tsaka da ayyukan ceto
- Aƙalla mutum 113 ne suka mutu sannan fiye da 4,000 suka jikkata
- Shugaban Ƙasa Michel Aoun ya ce hatsarin ya afku ne sakamakon fashewar tan 2,750 na sinadarin ammonium nitrate – wanda ake haɗa takin zamani da shi – bayan an ajiye shi ba tare da kulawa ba a wani wurin ajiya, bbchausa na ruwaito
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com