Zamfara : Ta’aziyya,Tambayoyi Da Gargadi !
Makon da ya wuce na jimami ne a jihar Zamfara. Matasa goma sha shida (16) a riwayar da ta fi yawa suka rasa rayuwar su a cikin hadarin mota. Matasan sanannu ne ga mutane da yawa. Ina mika ta’aziyya ga yan’uwa da abokaninsu. Allah Ya jikansu da rahama kuma Ya sa sun huta.
Alhini da jimami suna da muhimmanci kuma an yi su da yawa a wannan abun da ya faru. A matakin gwamnati, an yi zaman makoki na kwana uku. Wani abu mai muhimmanci da ba a yi ba shine magana akan wace irin tafiya ce tafito da wadannan matasa har hadarin ya auku? Ya hadarin ya auku? Akwai mai alhakin da ya kamata a tambaya diyya da sauransu? Mutun daya na ga ya je kusa ga wadannan tambayoyin, matashin dattijo Ibrahim Bello Marafa wanda na saka hoton hudubar da ya yiwa matasa a kan wannan al’amarin.
A duk lokacin da akayi hadari a gida ko a hanya, ina kokarin sanin menene ya kawo hadarin domin koyon darasi da hana faruwar irinsa.
Allah Ya yi muna hankali kuma Ya bamu umurnin “kada ku jefa kawunan ku zuwa ga halaka”. Ga dukkan alama, babban abinda ya kawo wannan hadarin shine al’adar fitowa tariyar Gwamnan Zamfara idan ya dawo daga tafiya. Na karanta ‘comments’ masu nuni da haka. Haka kuma, bayanin da mai magana da yawun gwamnati ya yi a kan rasuwar da turanci (wanda na sa hotonsa) na nuna kokarin nisantar da wannan alakar a lokaci guda kuma yana tabbatar da ita ga wadanda suka lakanci duba labari da zurfi. Ga wasu daga cikin abubuwan lura daga bayanin:
“Babbar mota ta kauce hanya ta kade kananan motoci guda hudu wanda ya kawo mutuwar fasinja goma sha hudu”
“Hadarin ya faru yan mintuna bayan Gwamna Bello Matawalle ya wuce wurin da abun ya faru daga tafiyar da ya gana da shugaban kasa”
Hankali na bamu cewa daurin aure kawai zai iya fitowa da matasa masu yawa da alaka a lokaci guda. Idan irin wannan ya faru domin tafiyar daurin aure, ba za a kira su ‘fasinja’ ba sai dai a ce “masu tafiyar daurin auren’. Idan ba daurin aure bane, to maganar tariyar Gwamna na da muhimmanci. Saboda haka, bai kamata a kira su “fasinja” ba sai dai ko “tawagar Gwamna” ko “yan tariyar Gwamna” wanda yana da banbanci mai yawa da kiran su fasinja domin zai karkatar da hakki da alhaki daga gwamnati.
A nazarina, jawabin da gwamnati ta fitar ya birkice komai. Maimakon daukar wani alhaki, sai gwamnati ta yi amfani da wannan ta nuna jinkan gwamna na komawa wajenda ‘fasinjan’ suka sami hadari daga ‘tafiyar sa ta ganawa da Shugaban Kasa’ sannan ya sa aka yiwa ‘fasinjan’ jana’iza ta alfarma kuma Ya bada umarnin zaman makokin mutuwar fasinjojin na kwana uku.
Muna iya tuna cewa wannan shine hadari na biyu mai alaka da tafiyar tawagar Gwamna. Na farkon ya faru minti kamar biyar kafin in iso wurin a hanyar Gusau zuwa Tsafe shima. Na ga gawawwaki tun kafin a saya su da haki. Daga cikin wadanda suka rasu inajin akwai dansandan tawagar Gwamna.
Da wannan nike kira ga Gwamnan jihar Zamfara da ya sauya abubuwa guda biyu. Na farko shine yanayin yanda ya ke tafiya da tawagarsa harda aikin yan tariya da rakkiya. Na biyu shine rage farfaganda ta hanyar da abu ya faru sai ayi sauri a fitar da jawabi na kauda hakikanin abu ga talakawa. Muna ganin haka akai-akai; ba da jimawa ba gwamnati itace kan gaba wajen karyata maganar da aka ce tsohon Babban Sufeton Yansanda ya yi a kan tsaro. Ga alama Gwamnan mu ya fi kowane Gwamna a Nijeriya kulawa da yada labarai; kamar yanda muka gani ma dai hirarsa ta musamman da BBC ta fi a kyarga cikin yanwatannin mulkinsa.
A karshe, rayuwa na da matukar muhimmanci. Gaskiya kuma ita ke mulkin al’umma fiye da komai. Mai mulki ya yi aikin da manema labarai za su neme shi ba ya neme su ba.
Madogara: caliphatepost