Labarai
Yanzu-Yanzu:Shugaban Boko Haram, Shekau ya saki Bidiyo inda ya tabbatar da bullar Boko Haram a jihar Naija
Advertisment
Rahota ni sun bayyana cewa a karin farko shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya saki bidiyo inda yake tabbatar da cewa sun hada kai da ‘yan bindigar jihar Naija.
Bidiyon ya bayyana inda yake nuna wasu da dama dake sallar Idi inda kuma suka mika sakon Barka da Sallah a yaren Hausa da Fulatanci da Turanci,jaridar hutudole na ruwaito.
Shahararren Lauya, Bulama Bukarti dake saka ido kan harkokin kungiyar ne ya bayyana haka inda yace wanda suka bayyana a Bidiyon an gansu sanye da kayan sojoji dana ‘yansanda, wanda hakan ke nuna cewa akwai yiyuwar sun kashe wasu jami’an tsarone suka samu wadannan kayan.
Yace idan dai wannan bidiyo ya tabbata to Boko Haram zata samu Dajin da zata rika buya kuma cikin sauki zata iya kai hari jihohin Kogi, Babban birnin tarayya, Abuja da Kwara.
Yace yana jawo hankalin gwamnatin tarayya data jihar Naija da su dauki wannan abin da gaske su kuma tabbatar an yi maganinsa ba sai ya kazanta ba a rasa yanda za’a yi.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com





