Addini

Masha Allah : Kwanan nan zamu kwato Masallacin Qudus daga hannun Yahudawa – Recep Tayyip Erdogan

Advertisment

A ‘yan kwanakin nan ne shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana cewa kasar Turkiyya tana shirin kwato Masallacin Al-Aqsa wanda aka fi sani da Masallacin Qudus daga hannun Yahudawa, kwanaki kadan bayan ya mayar da gidan tarihi na Hoghia Sophia Masallaci a ranar Juma’ar da ta gabata.presslive na ruwaito.

Shafin yanar gizo na shugaban kasar ya bayyana cewa kwato Masallacin ya samu hadin guiwar Musulman Hoghia Sophia. Ya ce hakan zai karawa Musulman da ake ciwa zarafi ake ketawa haddi karfin guiwa.

Wannan sanarwa ta shugaban kasar na Turkiyya, Erdogan, yayi alkawari kuma ya bayar da ‘yanci ga kowanne Musulmi dake alfahari da wuraren ibada dake karkashin wasu yankuna da aka kwace da karfi. Bayanin dai a takaice yana magana akan kwato Masallacin Al-Aqsa wanda yake a cikin kasar Isra’ila.

Amma hukumomin Masallacin na kasar Jordan, duk da haka kasar ta Isra’ila tafi karfi a Masallacin fiye da kasar Jordan. Wannan sanarwa dai an bayyanata ne da yaren kasar Turkiyya, inda aka fassara zuwa Turanci da Larabci.

Sanarwar da Larabci ta ce dawo da martabar Masallacin Hoghia Sophia “Kamar dawo da martabar Masallacin Al-Aqsa ne”, a takaice kwace Masallacin daga hannun Isra’ila dake cikin birnin Jerusalem, inda Masallacin yake.

Gwarzon Falasdinawa dai shine shugaban kasar Turkiyya, wanda a koda yaushe yake tashi tsaye don tallafa Falasdinawa da aka zalunta. Erdogan dai shine ya zama babban mai sukan Isra’ila akan cigaba da nuna zalunci da take yi kan al’ummar Musulmi.

Shugaban kasar yan son karawa Musulmai karfin guiwa musamman ma wadanda aka zalunta. Inda yake nuna musu cewa Musulmai na tare da su a koda yaushe.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button