Labarai

‘Yar Nijeriya Ta Farko Da Ta Fara Tuka Jirgi Mai Sukar Ungulu Na Yaki Ta Mutu

Advertisment

Daga Comr Abba Sani Pantami

Rundunar sojin sama ta Nijeriya ta sanar da mutuwar matukiyar jirgin sama Tolulope Arotile sakamakon hadarin mota a Kaduna.

Sanarwar da kakakin rundunar Ibikunle Daramola ya fitar ta ce Arotile ita ce mace ta farko da ta fara tuka helikwaftan yaƙi a Nijeriya wacce aka kaddamar a watan Satumban 2017.

Sanarwar ta ce matukiyar ta rasu ne a jiya Talata bayan gamuwa da hadarin mota inda ta samu munanan raunika a Kaduna.

Marigayiyar wace ƴar asalin jihar Kogi ce, an bayyana cewa ta bayar da gudunmuwa sosai a yaki da ƴan bindiga masu fashin daji a jihar Neja inda ita ce ke tuka jiragen rundunar Gama Aiki.

Babban hafsan sojin sama na Nijeriya Air Marshal Sadique Abubakar ya ce mutuwar jami’ar babban rashi ga rundunar tare da jajantawa iyalanta a madadin dukkanin jami’an rundunar sojin sama na Nijeriya.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button