Addini

Yadda Wasu Musulmi Suke Azumi A Garin Da Rana Ba Ta Faduwa

Garin Kiruna wanda yake da yawan Musulmi da suka kai 700, galibin jama’ar cikinsa masu sana’ar hakar ma’adanai ne. Garin yakan kasance a kewaye da tsaunukan kankara a lokacin bazara kuma yawancin mazaunansa baki ne wadanda aka baiwa mafakar siyasa.
Garin na karkashin kasar Sweden ne wadda take nahiyar Turai. A kowacce shekara rana kan kasance ba tare da ta fadi ba tsakanin ranakun 28 ga watan Mayu zuwa 16 ga watan Juli.
A lokacin da gidan talabijin din Aljazeera ya tuntubi wani mazaunin garin mai suna Ghassan Alankar, dan asalin kasar Siriya ya bayyana cewa
“Muna fara Sahur ne daga karfe 3:30 na asuba a wani yanayi mai cike da hasken rana. A lokacin nakan sanya labule guda biyu ne a tagar dakina saboda na rage hasken ranar da ke shigowa amma duk da haka haske ba ya fasa shiga cikin dakin.”
Al’ummar Musulmi da ke can suna yin azumin ne bisa dogaro da lokutan Sahur da Buda baki akalla guda hudu.
Mista Alankar ya ce yana azumin ne bisa dogaro da lokacin garin Makkah domin yin Sahur da kuma buda baki, a cewar sa, “saboda daga nan ne addinin Musulunci ya samo asali”.
Amma kuma ya bayyana damuwa cewa ko azuminsa zai samu karbuwa wajen Ubangiji ko kuma a’a.
Ko da yake bisa dogaro da Fatawar Majalisar Fatawa da Bincike kan Addinin Musulunci ta Nahiyar Turai (ECFR), yawancin masu azumin na dogaro ne da lokutan babban birnin kasar, Stockholm mai nisan Kilomita 1240 daga garin, domin daukar azumi da buda baki da kuma gabatar da salloli farillai biyar a kowacce rana.
A birnin Stockholm rana na fitowa da kuma faduwa kamar yadda ake samu a sauran wurare daban-daban na duniya.

#alummata

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button