Ganin Wata: Mu Yi Aiki Da ilimi Bayanin Farfesa Ahmad Murtala Mansur, Shugaban Sashin Nazarin Shariah da Addinin Muslunci, Jamiar Bayero Kano.
Da Sunan Allah Mai Raham, Mai Jin Ki. Allah ya yi Salati Mai taron Yawa ga Annabinmu Muhammad (Sallal Lahu alaihi wa sallam.
Bayan haka, Wasu sun turo da tambaya dazu a kan abinda ya faru da yammacin yau 29 Ramadan 1441H-22/05/2020. Wasu a Gashuwa ta Jihar Yobe da kuma Bauchi sun ce sun ga watan Shawwal. Sai dai da alama ba su isarwa da Sarkin Musulmi da wuri ba har ya yanke hukuncin cewa gobe Asabar za a karasa azumi na 30. Tambayar ita ce ya ya mutanen da suka gani zasu yi? Sannan kuma wanda suka fadawa ko ya gasgata su a gane da labarin sun gani ya ya zai yi goben, zai azumi ko kuwa?!
Amsa: Alhamdulillah. A Musulunci Idan hukuma ba ta karbi bayanin wani mutum a ganin wata ba, za a bi abinda hukuma da take kula da dauka da sauke azumi da bayanin salla karama da babba ta yarda da shi. Mas’alar sananniya ce ko an Kasar ma. Amma a wurin malamai akwai magana uku:
a-Mutumin da ya gani ba zai sauke ba gabadaya don toshe kafa kada wasu su mayar da abin wasa. Wannan shi ne abinda Imamu Malik ya fada a Muwadda. Shi ne kuma bayanin da Imamu Abu Hanifa da Imamu Ahmad bn Hanbal suka tafi a kai.
b-Akwai masu ganin zai kame a zahiri amma zai yi niyyar saukewa. Wannan shi ne ra’ayin Ash’hab da Jallab daga Malikiyya. Shi me kuma ra’ayin Shafi’iyya.
c-Wanda ya san ba za a kama shi ba don zai yi kamar tafiya da sauransu sai ya sha, wanda kuwa ya san za a cimma sa sai ya hakuri ya bi al’umma.(Minahijut Tahsili na Abul Hasanil Rajraji Al-Maliki; Maj’mu’ul Fatawa na Ibn Taimiyya).
Amma a gakiya, maganar farko ta fi dalilai masu karfi. Domin Abdullahi bn Umar ya ce: Mutane sun nemi wata sai ni na ganshi, sai na fadawa annabi sai ya yi azumin. Ya kuma umarci mutane da su yi”. (Abu Dawuda da Darimi). Wannan ya nuna cewa ana isarwa da hukuma. Sannan malamai da yawa sun dauki ganin wata a matsayin Shaidan ba labari ba kurum. Don haka sai an isar da shi ga hukuma ta tabbatar da shi Sannan a yi aiki da shi.
Akwai bayanai masu yawa daga malamai da za su dada tabbatar da abinda aka fada. Ga wasu daga ciki:
i-A lokacin Sayyadina Umar wasu mutane su biyu suka ga wata na sauke azumi. Kafin su je su sanar sai dayan ya fara shan ruwa. Sai Sayyadina Umar ya ce da shi: badanan dan’uwanka ba da na zaneka.-(Sunanul Baihaki). Yana nufin bai kawo abin gaban Shugaba ya tabbatar ba.
iiAi’sha Matar Annabi tana cewa: Ranar Babbar salla ita ce wadda mutane suka hadu suke yin salla. Ranar karamar salla ita wadda mutane suka hadu cewa ita ce karamar salla”.-(Sunanul Baihaki).
iii-Manyan malamai na tabi’ai kamar su Hasanul Basari da Muhammad bn Sirina da Mujahid duka suna cewa : “Daukar azumi da sauke shi yana tare da jama’a ne da yawancin mutane”.-(Al-Mugni na Ibn Kudam).
iv-Amru bn Muhajir ya ruwaito cewa “Muhammad bn Suwaiba Al-Fihri ya sauke azumi kafin sauran mutane! Sai Umar bn Abdul’aziz ya rubuta masa wasika cewa: Menene ya dauke ka ka sauke azumi kafin sauran mutane!? Sai ya ce: Hizamu bn Hakimu bn Hizam ne y shaida mini Cewa ya ga wata! Sai Umar bn Abdul’aziz ya aika masa da cewa: Kai a daraja ka ke darajar Zul-Yadaini ne?!”(Musannaf na Ibn Abi Shaiba). Zul-Yadaini shi ne wanda ya ga Annabi ya yi rafkanuwa a Salla sai ya fada Annabi. Amma Annabi bai gamsu ba sai da ya tambayi mutane suka dada tabbatar da an yi rafkanuwar, sannan ya yi sujjadar rafkanuwa. A nan Umar bn Abdul’aziz ya so ya ce da shi dole sai an tabbatar sosai kafin a zartar ko a karba.
v-Abdullahi dan Imamu Ahmad bn Hanbal ya ce na tambayi babana a kan wani ya ga wata ya ya za a yi?! Sai ya ce: Shugaba shi ne zai Umarci mutane su dauki azumi”-(Masa’ilu Ahmad)
vi-A aikace kuma Imam Ahmad din yana yin haka. Domin duk lokacin da wata Ramadan ya zo 29, sai ya yi sallar Isha. Sannan ya aika gidan shugaba yana neman labari. Idan an shaida masa an gani shi kenan. Idan kuma ba a gani ba l, ya tashi da azumi gobe. (Bada’i’ul Fawa’idi na Ibnul Kayyim). Har an ruwaito Imamu Ahmad bn Hanbal din yana cewa: “Babbar salla da karamar salla duka suna ga Shugaba ne. Idan ya ajiye azumi, sai mutane su ajiye. Idan ya yi babbar salla sai mutane su yi. Haka nan Idan ya yi sallar idi, sai mutane su yi”. (Assunnah na Abubakar Al-Khallal).
vii-Haka nan Imamu Ibn Nujaim a Mazahabin Hanafiyya ya fada a cikin (Al-Bahrur Ra’ik). Haka nan Al-Qadi Abdulwahab Al-Maliki a cikin (Attalkinu) ya tabbatar da haka.
viii-Shehul Islami Ibn Taimiyya yana cewa: “Idan mutumin da ana iya dogara da shi a tabbatar da wata, ya ga watan Zul-Hijja amma sai shugaba bai karba ba saboda wani uzuri na zahiri ko kuma ma wata gazawar shugaban a game da tabbatar da ganin watan, sai Ibn Taimiyyan ya ce: wannan mas’alar za a iya fitar mata da hukunci a kan sabanin nan mashahuri na mas’alar wanda ya kaita da ganin wata Shawwal. Sai ya kawo maganganu guda biyu irin wadanda muka fada tun farko.-(Al-Ikhtiyarat Al-Fikhiyya na Al-Ba’li). Muhimmi dai koda akwai wata gazawa daga bangaren shugabanni wajen tabbatar da ganin watan, to sai dai a karbi hukuncinsu, ba za a tsaya tada jijiyar wuya ba!
Sai dai duka malaman mazahabobin suna cewa wanda ya gani ba a karba ba, amma kuma ba shi da lafiya ko wani kwakkwaran uzuri zai iya sha ba sai kuma ya rama ba. Shi kuma wanda ya sha da ganganci, yana ganin ai shi ya ga wata amma an ki a karba, to sai ya rama tare da kaffara a gurin malaman Mazahabin Malikiyya. Idan kuma ya yi ne da jahilci, to suna cewa sai ya rama a magana mafi karfi.-(Annawadiru Waz Ziydat na Ibn Abu Zaidin Al-Kairawai; Sharhin Tafri’i na Attannukhi; Raudatul Mustabin na Ibnu Bazizah; Attaudihu na Khalil bn Ishaka, Hashiyatud Dasuki).
A karshe, duk wanda ya gani amma ba a karba ba, idan ya yi azumi a wannan rana, to ba shi da laifi. Domin wannan ranar ba ita ce ranar idi ba saboda ba ta tabbata a matsayin idi ba. -(Majmu’ul Fatawa na Ibnu Taimiyya).
Wadanda suke cewa sun gani a Yobe da Bauchi da sauransu tunda basu isar da bayaninsu ba ga hukuma har ta zartar da hukunci, sai su hakura a yi azumi gobe tare da su. Wannan shi ne bayani mafi alheri insha’allah. Sannan ba fa yau ne aka fara yin haka ba a nan Kasar. Mutane ne suke mantawa ko kuma wadanda suka yi wayo yanzu. Sannan kuma a zamanin yanzu ga social media tana hannun kowa!!
Malaman da suke bugar kirji su ce mutane su fito su yi idi saboda an sami bayanan an ga wata a wasu wurare, fitina suke so su kawo. Domin abinda suke ba shi ne koyarwar magabatan malamai kamar yadda aka kawo bayanin hakan a sama. Duk cikinsu ba bu shugaba, ba hukuma, ba su ne Sarkin Musulmi ba. Don haka, za a kyalesu a bi abinda hukuma ta tabbatar. Duk cikinsu ba wanda zai kawo wata fassara a aikace da malaman wannan al’umma na farko suka tafi a kan irin wannan fitinar da suke son su kawo da fadada sabani tsakanin Musulmi. Sai dai su kawo nassoshin da su da kansu ko dai ba su san fassara magabatanmu kwarai da suka yi musu ba, ko kuma son a ce sun sabawa hukuma ya yi katutu a zukatansu. Allah ya kyauta!
Sayyadina Usman ya cika salla a filin Arfa saboda ya ganin yana da iyali a Makka don haka ba dole sai ya yi raka’a biyu ba. Abdullahi bn Mas’ud ya ce wannan ba shi yi ne Sunna ba. Amma da aka zo yin sallar sai ya bi shi a ka yi raka’a’ hudu. Sai aka tambayeshi don menene ka bi shi, sai ya ce: “Sabani Sharri ne !”-(Abu Dawuda). A kan wannan zamu rika duba abubuwa a karkashin hasken ayyukan magabata, ba hauma-haumar ‘yan son a saba ba tare da an zauna an tattauna da hukumomi an fito da mas’aloli a kan tebur ba!
A dunkule, sai a yi hakuri, mu sami ladan azumin gobe. Allah ya sa mu dace!Da Sunan Allah Mai Raham, Mai Jin Ki
All
ah ya yi Salati Mai taron Yawa ga Annabinmu Muhammad (Sallal Lahu alaihi wa sallam.





