Addini

Ka Da Allah Ya Jarrabe Mu Da Yin Nadama Bayin Barin Ka Mulkin Najeriya – Martanin Sheikh Adam Albani Gombe Ga Buhari

Advertisment

Ka Da Allah Ya Jarrabe Mu Da Yin Nadama Bayin Barin Ka Mulkin Najeriya - Martanin Sheikh Adam Albani Gombe Ga Buhari
Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan da ke garin Gombe, Sheikh Muhammad Adam Auwal Albani, ya fito ya yi martani ga shugaban Ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari, game da wani furuci da ya yi, in da ya ke nuna, ƴan alhinin rabuwa da shi da ƴan Najeriya za su yi, idan wa’adin mulkin sa ya yi.
Akan wannan ne a yayin wata huɗubar Juma’ar da ya gabatar a makon da ya gabata a masallacin Bolari da ya ke Limanci a garin Gombe, Sheikh Adam Albanin, ya nusar da shugaban kan abubuwan da ya furta wanda ya ce babu abun da ya ke cikin su sai tarin kuskure da kuma yi Ƙasar mummunar fata.
Domin kamar yadda Malamin ya nuna, wannan kalami bai kamata ya fito daga bakin mutum kamar Shugaban Ƙasa ba, kuma ya yi kira ga shugaban akan ya gaggauta fitowa ya janye waɗannan munanan kalaman na shi in dai ya na nufin Kasar da yankin sa na Arewa da alheri a matsayin sa na Musulmi.
Haka nan kuma Malamin ya bayyana yadda Shugaban ya yi watsi da yankin Arewa, yayin da ya ke ta zubawa ƴan Kudu kuma ayyuka rututu. Domin ya yi bugi kirjin cewa, idan akwai wani aiki guda ɗaya tilo muhimmi da shugaban ya ɗauko ya kuma kammala a yankin Arewa, ya na son a nuna masa.
Ga cikakken bayanin na shi a cikin wannan bidiyon
https://youtu.be/En4i9pIvbJI
 

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button