Addini

CORONA VIRUS: Malamai Sun Yi Gaggawa Wajen Bada Fatawar Rufe Masallatai, Inji Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zariya

Advertisment

“Kafin malamai su bada fatawar hallacin rufe masallatai saboda gudun yaduwar cutar corona virua ya kamata su zurfafa wajen bibiyar hanyoyi da dalilan da ke yada wannan cuta da kuma yadda za a kauce wa yaduwar ta, da a ce sun zurfafa bincike akan haka da ba su yi saurin bada fatawar rufe masallatai ba saboda dalilai kamar haka:

Dalili na farko, masana lafiya sun tabbatar da cewa idan aka bada tazarar mita biyu a tsakanin juna za’a kaucewa hadarin kamuwa da wannan cuta, a nan tunda akwai zabi ba mu da hanzarin barin jam’in salla saboda tsoron cuta, maimakon a bar jam’in salla gara ayi jam’in ba yanda aka saba ba ta hanyar ba da tazarar mita biyu da juna a sahu maimakon a bar jam’in kwata kwata.

Dalili na biyu, idan muka gwada wannan kadiyyar da kadiyar sallar tsoro (Salatul Khaufi) zamu ga cewa babu wani tsanani ko fargaba ko tsoron da zai sa abar jam’in salla matukar za’a iya gudanar da jam’in koda ya saba da yanda aka saba yi.

Allah ya saukar muna da aya na musamman a cikin Alqur’ani wanda take bayani akan sallar tsoro, dalilin saukar ayar shine, ana cikin yaki kafirai suka ce mu jira akwai wani salla da muminai suke yi idan suna wannan sallar sukan bar komai, mu kuma sai muyi amfani da wannan damar mu afka musu sai Allah ya saukar da ayar (فإذا كنت فيهم فأقمت لهم الصلاة) har zuwa karshe, inda yake bayani akan yanda za’ayi sallar tsoro dan kare rayuka, bayanin yanda ake sallar tsoro yana nan a cikin littafan Fiqhu.

Yanda Ake Sallar Tsoro (Salatu Khaufi)

Sarki ko liman zai kasa mayaka gida biyu, kaso na farko za su yi raka’ar farko tare da liman, na biyu kuma su rike makami suna bada kariya, bayan liman ya cika raka’a daya da kaso na farko, sai ya mike yayi musu ishara da su cika sallarsu, idan suka cika, sai su dauki makami su ci gaba da bada tsaro sannan dayan kason su zo liman ya karasa raka’a ta biyu da su, idan ya zauna zaman tahiya sai yayi sallama su kuma suka tashi su cika sallarsu.

A nan kadiyyar sallar tsoro (Salatul Khaufi) ya bada fa’idar cewa tsanani tsoro ko firgici ko cuta bai hallata a bar jam’in salla matukar akwai damar da za’a iya yin jam’in.

Allah ya sakawa malaman wasu kasashe da suka fadakar da gwamnatocinsu suka bari aka rinka gabatar da sallolin jam’i cikin tsari da bin ka’idoji maimakon hana jam’in kwata kwata.

Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zariya shine
(Mataimakin Shugaban Kungiyar Fityanul Islam Na Kasa)

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button