Nima Na Fice Daga Kannywood – Jaruma Asma’u Nass
Fitacciyar jaruma a cikin masana’antar Kannywood, Asma’u Ahmad wadda a ka fi sanin ta da suna Asmau Nass ta bayyana cewar ta fita daga cikin Kannywood.
Jarumar ta bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da majiyar mu ta yi da ita game da wannan furucin na ficewa daga masana’antar.
Mun kuma fara tambayar ta kamar haka, kwana biyu ba a jin duriyar ki a fina-finai, karatu ne ya boye ki ko kuwa kin bar harkar ne baki daya?
Jarumar ta ce “A gaskiya karatu ne ya boye ni daga harkar fim, domin tun a shekarar bara da na shiga ajin karshe a makaranta na dan ja jiki na, saboda ina son na mayar da hankali na a kan abu guda daya gaskiya, kuma bayan da na kammala karatu ban koma ba gaskiya, ba don ba na so ba, sai dai kawai kamar yadda na fada mi ki a baya na fi son na tun kari karatu na da kuma ci gaban rayuwa ta. Maganar gaskiya shi ne na dai na fitowa baki daya, duk wani abu da ya danganci harkar fitowa a gaban abun daukar hoto na bar shi gaskiya, na sha samun waya da sako daga mutane da dama su na tambayar ina na shiga ba a jin duriya ta ne? Sai dai in ce ina nan, amma maganar gaskiya na dai na yin fim kwata- kwata a yanzu”. Inji Asma’u Nass.
Idan jarumai za su yi karatu su kan hada da harkar su ta fim, a bangaren ki mun ga ba hakan ya ke ba, sakamakon wannan hukuncin da ki ka dauka?
“Eh to gaskiya karatun da na yi ba a kan harkar fim ba ne, tun da kan na fara fim na fara karatu na, abun da na karanta bai shafi fim ba. Shi fim kawai na dauke shi ne kamar abun sha’awa, amma ba ni da alaka da shi ta bangaren karatuna”.
Wane lokaci ki ke sa ran yin aure?
“Kin san shi aure babu wata mace a duniya da za ta ce ba ta da burin yin aure gaskiya, kuma ni ma a nawa bangaren hakan ya ke, mutane da dama sun yi mun wannan tambayar, kuma kullum amsa ta guda daya ce, nakan ce nan ba da jimawa ba. Abu daya nasan cewa shi aure da ki ke gani lokaci ne, idan lokacin sa ya yi ko ka shirya ko ba ka shirya ba za ka yi shi”.
“Wace shawara za ki baiwa jarumai da sauran mutanen da ki ka bari a baya, ina nufin wadanda ki ka bari a cikin masana’antar ta Kannywood.
“Shawara ta guda daya ce a gare su, kawai su ji tsoron Allah su kuma rike gaskiya, to Allah zai dafa musu”. A cewar Asma’u Nass.







