Mutuwar saurayina ce ta sa nayi wakar “Mai Nema” – Maryam A. Sadik


Mawakiya Maryam A. Sadik ta ce ta yi wakar “Mai Nema…” ne saboda jan hankalin iyaye musamman a Hadejia game da al’adar lallai sai mai gidan kansa za a bai wa Aure.
Ta ce ita Saurayin da take tsantsar kauna, ya rasu bai samu ya yi gidan ba, ballantana su yi aure.
Maryam ta bayyana hakan ne filin “Fitattun Mawaka” na tashar Dala FM Kano.


Maryam Abubakar sadiq wanda anka fi sani maryam a.sadiq mawakiya ce wanda tayi wakar “nema” wakar nema tayi ita kadai kuma tayi tare da fasihin mawakin nan sadiq saleh.
Maryam a sadiq a cikin tattaunawa da tayi da Dala fm Kano inda ta fadi kadan daga cikin tarihin rayuwarta
Dalilin da yasa nayi wakar mai nema.
“To abinda yasa nayi wannan wakar shi saurayina nura da na baka labari malamain makaranta ne ta kudi sai yazo ya same ni yace maryam idan ke samu wanda yake sonki ya shirya aure ki aure shi, sakamakon ni yanzu banda hali ko fili bani da shi kuma mu al’adarmu ce ta hadejawa , idan baka da gidan kanka da wuya a dauki mace a baka a aura maka ita
Sai nace masa to ae wannan abu ne na Ubangiji a yanzu ma zaka iya samu yace a’a shidai zaifi masa daɗi idan ina da tsayaye naje na aure shi a lokacin naji maganar tasa nace masa amma dai ae ba rabuwa zamuyi ba , idan kai dine ko wani Allah ne ya barwa kansa sani.
ina cikin haka da shi banyi auren ba ma sai Allah yayi masa rasuwa , ina so na nunawa iyayenmu samu da rashi na Allah ne.
Zaka iya aurawa mai kuɗin yarka kuma a wayi gari bashi da shi, zaka iya aurawa talaka yarka suyi arziki tare kaima kaga wannan abun farin ciki ne a wajenka – inji maryam.”
Shafin Dala fm kano na YouTube ne sunka wallafa bidiyon.
Ga bidiyon nan.