Labarai

Ina Sa Ran Abba Kyari Ya Yi shahada – Sheikh Isa Pantami

Sheik Isa Ali Pantami ya ce babu abin da ya kamata mutane su yi illa su yi wa Malam Abba Kyari addu’a saboda yanayin halin da ake ciki na annobar cutar korona, yana mai cewa ba sai an je zaman makoki ba.
Pantami wanda ya jagoranci addu’a a wurin bimne Abba Kyari, ya ce ana kyautata zaton Abba ya yi shahada.
“Manzon Allah S.A.W. ya ce yana daga cikin kyakkyawan karshe mutum ya mutu ranar Juma’a sannan wanda annoba ta kashe shi yana mai imani shi ma dan Aljanna ne,” in ji Pantami.
Ya kara da cewa saboda kiran da kwararru suka yi na bayar da tazara, ya kamata kowa ya tafi harkokinsa bayan binne shi.
“Daga nan wurin an sallami kowa, ba sai an je wurin karbar gaisuwa ba saboda da ma karbar gaisuwa din al’ada ne.”
An binne Malam Abba Kyari ne a makabartar yankin Gudu da ke Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja bayan an kai gawarsa daga Jihar Legas, inda ya mutu bayan jinyar cutar korona.
Article share tools

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button