Tabarikkah: Ahmed musa ya gwangwajewa mutane 4 gida a abuja harda mai gadinsa
A ƙoƙarin da ya saba yi wajen tallafawa al’umma, shahararren ɗan ƙwallon ƙafan Najeriya, Kaftin Ahmed Musa MON ya gwangwaje wasu mutane da kyautar gidaje domin su samu muhallin zama da iyalansu, shafin dokin karfe na wallafa a shafinsu na sada zumunta.
Daga cikin mutanen da suka samu gidan akwai mai gadinsa wanda ya ba shi gida mai ɗaki ɗaya, da P.A ɗinsa wanda ke zaman abokinsa shi ma ya samu gida mai ɗaki uku, da kuma ma’aikacin ƙungiyar ƙwallon ƙafa shi ma ya samu kyautar gida mai ɗaki uku, sai kuma wata ƴar Jarida wacce suka daɗe tare tun yana ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ita ma ya gwangwaje ta da gida mai ɗaki biyu.
Kaftin Ahmed Musa mutum ne gwarzo wanda ya daɗe yana sanya farin ciki da walwala a cikin zukatan al’umma daban-daban. Ko da a baya-bayan nan ya gwangwaje tsohon ɗan wasan Hausan nan Baba Karkuzo da kyautar gida, ya kuma sanyawa wasu abokansa tun na ƙuruciya gida kyauta ya ba su.
Akwai mutane da dama da suka rabauta da samun gida a sanadiyyarsa, wasu kuma ya tallafa musu ne ta fuskar ilimi, abinci da jarin dogaro da kai da dai sauran muhimman fannoni rayuwa daban-daban. Wanda a sanadiyyar hakan ɗumbin al’umma na cigaba da yi masa godiya da addu’ar fatan alkhairi.
Wani labari : Da dumi’dumi: Hafsat ta musanta aika Nafi’u Lahira a gaban kotu
Matashiya Mai suna Hafsat surajo ta shadawa alkalin Kotun Majistri a Kano cewar ba ita ce ta hallaka abokinta na kusa kusa Nafi’u ba.
Idan Baku manta Da farki dai Hafsat ta shaidawa ‘Yan sanda cewa ita ce ta kashe Nafi’u shi bayan ya hana ta kashe kan ta amma yau ta musanta hakan a gaban kotu.
Kotun ta aike da Hafsat Zuwa gidan kurkuku kafin zama na gaba.