Kannywood

Kungiyata Zata Bada Tallafin Kayan Abinci A kano – Fauziyya D Suleiman

Advertisment

Kungiyar CHNF wato Creative Helping Needy Foundation ta fitacciyar marubuciyar litattafan Hausa, Fauziyya D Suleiman ta ce za ta bada tallafin kayan abinci a jihar Kano ga talakawa marasa karfi sakamakon rufe jihar Kano da za a yi kan cutar Covid-19.

Shugabar kungiyar, Fauziya D Suleiman wadda ta yi suna wajen tallafawa marasa karfi ta hanyar ba su jari da samar da mafita a lokacin da al’umma ke cikin bukatar taimako domin ganin kungiyar ta bada tallafin ta.

Marubuciyar ta bayyana hakan ne a shafin ta na sada zumunta wanda wasu daga cikin al’umma su ka yi kokarin kawo na su tallafi, wanda yawanci tallafin an fi kawo shi ne a lokacin azumi, amma wannan karon tun kafin azumi kayan su ka karaso.

Marubuciyar ta bayyana a shafin sadarwa na instagram inda ta ce “ Alhamdulillahi abincin da mu ka kara siya kenan, za mu yi iya bakin kokarin mu ga ‘yan Kano, amma Allah ya san sauran jihohi irin su Kaduna, Katina, Jos da dai sauran su, ba za mu iya taimaka mu su ba a halin yanzu, muna kira ga masu hali da su ke wadandan garuruwan da su dubi Allah su taimaka, muna da wakilai da za a iya bawa su rabawa wadanda su ke cikin tsananin bukata. Allah ya sakawa masu taimakawa da alkhairi”. A

Cewar Fauziya.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button