Kannywood

Burina Da Addu’a ta Kullum Shine Na Ga Matan Kannywood Allah Ya Kawo Musu Mazaje Duka Su Yi Aure – Abubakar Maishadda

Advertisment

Burina Da Addu'a ta Kullum Shine Na Ga Matan Kannywood Allah Ya Kawo Musu Mazaje Duka Su Yi Aure - Abubakar MaishaddaA cewar fitaccen Furodusa a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Abubakar Bashir Maishadda: “Don Allah duk wata yarinya budurwa ko wacce ta taɓa Aure da ta ke da niyya ko son shiga harkar Fim ta yi haƙuri, ta je ta yi karatu ko ta nemi wata harkar daban, idan kuma ta samu miji ta yi aure ya fi mata.”
Game da jarumai mata da ke cikin harkar kuwa, a dai cikin zantawar mu da Furodusa MaiShaddan, ya bayyana cewa: “…Yanzu ma harkar a cike take. Suma jaruman (mata) duka fata na ke yi Allah Ya kawo musu mazan Aure, su yi, su tafi ɗakunan su…
…Don ba abun da ya fi dacewa da mace kamar ɗakin ta. Kuma kullum a cikin ba su shawara na ke kan in su ka samu mazan Aure, su yi domin shine mutuncin su.”
Domin sauraron cikakkiyar hirar mu da MaiShaddan kan wannan matsaya ta shi game da ƴan matan Fim ɗin,
Gata nan.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button