Kannywood

A kai na dokokin Afakallah ke ƙarewa, inji Adam Zango

Advertisment

Abin da ya sa na yi rajista da hukuma’

ADAM A. Zango ya amayar da abin da ke cikin cikin sa game da dangantakar sa da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, ya na faɗin wasu dokokin hukumar ma saboda shi ake ƙirƙiro su.

A wata hira da ya yi da gidan rediyon BBC Hausa, fitaccen jarumin kuma mawaƙi ya kuma bayyana dalilin sa na yin rajista da hukumar, wadda ke ƙarƙashin shugabancin Alh. Isma’il Na’abba (Afakallah).

Ya ce ya yi rajistar ne ba domin komai ba sai saboda yaran sa su rinƙa samun aikin shirya finafinai.

A cewar sa, an daina gayyatar yaran nasa zuwa aikin shirya fim tun bayan lokacin da ya bayyana ficewar sa daga Kannywood.

Mujallar Fim ta ruwaito Zango ya yi bayani kamar haka: “Na dawo na yi rajista da Hukumar Tace Finafinai ne a dalilai guda biyu. Na farko shi ne furodusas ɗi na da su ke fim da ni, a Kano sun fi yawa kuma yara na da na ke zaune da su, na ke mu’amala da su, abokai na duka, su na samun matsala, ba a kiran su ayyuka a dalilin waɗannan abubuwa da ban yi ba.

“Wasu ma sun yi rajista, amma saboda su na tare da ni ba sa samun ayyuka.

“To sai na ga menene dalilin da ba zan yi ba? Idan na yi, ba don wani kuɗin shiga wai da zan ce na yi ba. Amma me zai hana na yi? Don waɗannan mutanen sun daɗe su na bibiya ta.

“Magana ta gaskiya, ban taɓa zama na yi tunanin hakan ba; sai a ‘yan kwanakin nan da su ka wuce ne na ga cewar to waɗannan mutanen gaskiya kamar na shiga haƙƙin su ne, saboda su na yin finafinai da ni.

“A ciki akwai wanda ba ya yin fim da wani jarumi sai ni, amma a dalilin ban yi rajista ba ya haƙura ya daina.”

Ya ci gaba da cewa: “Sai su ka rinƙa yin ayyukan da wasu jarumai, amma kuma jaruman su na ba su matsala, su na cika musu kuɗi, su na yi musu wulaƙanci, wanda hakan ya sa ban ji daɗi ba.

“In da kamar a ce na yi rajista, kenan ba za a samu wannan matsala ba.

“Daga baya na yi tunani na ce bari in je na yi rajistar.”

Zango ya yi gargaɗin cewa kada fa a ɗauka ya dawo cikin masana’antar finafinan Hausa ne.

Ya ce: “Kuma hakan ba shi ne ya nuna na dawo Kannywood ba. Har yanzu ina nan a matsayi na na mai cin gashin kan sa, saboda hukumar ba ta ce dole sai ka na ƙarƙashin Kannywood za ka je ka yi rajista ba.”

A cewar sa, “Ina so mutane su  san cewar dangantaka ta da abokan sana’a ta ya na nan, ba ni da wata matsala da kowa, ƙungiya ce ta Kannywood da ba za ta iya ƙwato mini ‘yanci na ba na ce na daina, ba na yi!”

Dangane da dokokin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano kuwa, a nan ne jarumin ya yi kakkausar suka, ya yi nuni da cewa ana bambanta shi da sauran ‘yan fim.

Zango ya ce: “Ƙa’idojin da hukumar ta gindaya ya na kan dukkan jarumai da mawaƙa da su ka yi rajista. Nawa ba zai bambanta da na kowa ba, duk da dai wasu lokutan dokokin da ya ke kai na bai kan kowanne jarumi.

“Kamar yadda aka yi a kwanaki na haska fim ɗin Rahama Sadau, ka ga ai wannan Rahama kan ta ma ba ta da rajista, amma ta kira masoyan ta su zo su kalli fim, ta yi tallan fim ɗin ta kuma an zo an kalla.

“Amma ni zuwa zan yi, ba ni da alaƙa da fim ɗin, jarumi ne kawai ni, zan zo na ba ta gudunmawa ne na kira jama’a su zo su kalla, (amna) aka dakatar da ni.

“To ka ga doka ne ba a kan kowanne jarumi ba, nawa daban ne.

“Ita Rahama fim ɗin ta ne fa, kuɗin sule biyar ba zai shiga aljihu na ba a matsayi na na Adam A. Zango.”

Haka kuma jarumin ya faɗi dalilin sa na ƙin yin rajista da hukumar tun da farko.

Ya ce, “Abin da ya hana ni yin rajista, lokacin da zan yi wasan Sallah, ina so ka sani cewar a kai na ma aka ƙirƙiro rajista, saboda lokacin da zan yi wasa na na Sallah su ka dakatar da ni cewar ba zan yi wasa ba sai na je na nemi izini, bayan a lokacin na san jarumai da yawa sun yi wasa a Jihar Kano ba tare da sun nemi izini ba.

“Tun da aka kafa hukumar ba wanda ya je ya yi rajista shi kaɗai a matsayin sa na jarumi, sai a kai na aka fara.

“Sai na ce tunda babu wanda ya je ya yi, to ni ma ba zan yi ba. Su ka ce ba zan yi wasa ba, ni kuma na ce to na haƙura.”

A ƙarshe, ya bayyana nadama kan yadda aka kasa gane irin gudunmawar da ya bayar ga cigaban Kannywood.

“Mutanen da su ke cikin masana’antar – shugabannin mu da waɗanda ake tare – sun riga sun san irin gudunmawar da na bayar,” inji shi.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button