Uncategorized

Ni Budurwa ce Amma WallahiNi Da Namiji ce Bazan Auri Budurwa Ba ,Bazawara Zan Aura – Zainab Ali

JARIDAR DIMOKURADIYYA:Wallahi Allah ni Budurwa ce amma tsakani da Allah ni da Namiji ce da bazan Auri Budurwa ba Bazawara zan Aura.

Wata Budurwa Yar kimanin Shekaru Goma sha Tara 19 mai suna Zainab Ali ta baiyyanawa Wakilin mu Shuaibu Abdullahi cewar wallahi ita da Allah ya halicceta a Namiji bazata Auri Budurwa ba Bazawara zata Aura.

Zainab Ali tace gwara in Auri Bazawara in san dama chan bazan taba samun ta kamar budurwa ba, amma tashin hankalin da kokwanto zai biyo baya ne idan ka Auri Budurwa kuma ka sameta ba yadda kake tunani ba.

Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa Zainab tace yanzu sai kayi da gaske kai iya bayar da shedar Yayar ka ko Kanwarka ko Yarka saboda halin da zamani ya riski Yan Mata.

Yanzu abun haushi sai kaji Maza suna cewa ga Yan mata nan da yawa sai wacce ka zaba, kuma duk wani kwadayi da zai jefa Budurwa a cikin Shashanci baya wuce Siyan Waya da kuma kudin Anko, haka kuma idan Namiji ya sami damar yin Lalata da Budurwa sai ya baiwa Abokin shi labari ba zai rike mata sirrin ta ba.

Ba cewa nayi babu Yan matan Kwarai ba to amma sai mutun yayi da gaske.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button