Uncategorized

AL’AJABI: Budurwa Ta Bankawa Kanta Wuta A Garin Gusau Saboda Saurayinta Ba Shi Da Kudin Aurenta

Daga Mashkur Abdullahi Tsafe

Wata yarinya mai suna Aisha dake anguwar Albarkarwa dake nan garin Gusau jihar Zamfara ta yaiyafawa kanta fetur ta kestawa kanta ashana.

Wannan alamari ya farune jiya assabar, a anguwar albarkawa gusau

A zantawarmu da mai unguwar anguwar Alh Aminu Muhammad ya shaida mana cewar lokacin da abun ya faru yarinyar ta fito waje tana kururuwa na neman agaji a waje yayin da su matasa suka yi kanta tare da kashe mata wutar da tu ni ta ci zarafinta.

Yayin zantawarmu da Aisha ta bayyana mana cewar ta dauki wannan mataki ne sanadiyar saurayin ta ba shi da kuddin auren ta kuma iyayensa ba su da hali ita kuma saboda zumudi irin na soyyaya ta ga da ta aikata zina gara ta kashe kanta duk da yake ta san kisan kai babban laifi ne.

Yanzun haka dai wannan boyar Allah tana nan kwance rai kwa-kwai mutu kwa-kwai a gidansu sanadiyar rashin kudin zuwa asibiti.

Kamar yadda Mai Unguwar shiyar ya shaidawa manema labaru ko da abun ya faru naira 750 kacal ne a gidan don haka ba zarafin zuwa asibiti da wannan ake neman masu tausayi kuma masu hali za su ceto rayuwar Malama Aisha.

Dafatar Allah yakaremu da aikata aikin dana sani.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button