Uncategorized

Yadda Ake Sace Zuciyar Mace

Farkon Haduwarku: Yanzu lokaci ya canza an daina furtawa ‘yan mata kalmar so a haduwar farko, lallai ne idan kana so ka samu karbuwa wajen mace, to ka samu wata hanya wadda za ku tunga haduwa kuna fira. A cikin firar ka da ka kuskura ka nuna mata alamomin so, ka kyale ta zuwa gaba za ta sani, ka yi kokarin saka ta dariya a lokacin da kuke tare. Idan kuka fara shakuwa ka ringa nuna mata duk duniya ba ka ga macen da ta tsaru ba kamar ta, amma ka da ka zake a wannan fannin. Sannu a hankali sai ka fara aika mata sakon wasika ta ido kuma zuwa lokacin ka dan ringa tambayar ta cewa, wai waye mai tsananin sa’a ne ya mallaki zuciyar wannan tsadaddiyar yarinyar ?
Idan har ta basar da zancen, tofa kaci gari ko kuma ta ce ma wani ne kuma ta ki fada maka sunansa to kai din take nufi.
Akwai wasu halaye da ya kamata ka daina lokacin da za ka je wajen mace, domin neman soyayyar ta da kuma lokacin da ka zama wanda take so. Halayen su ne kamar haka:
•Yawan tambaya, mai yawan halayya na tambaya ya kan saurin fita daga zuciyar mace.
– Ka sani dole ne ka dan yiwa wacce kake so hidima ko da kuwa ba auren ta za ka yi ba, domin kuwa mata ba su son marowacin saurayi.
•Idan ka tabbata ka zama wanda take so sosai, to kaima sai ka dan ja na ka ajin. Kamar ka daina bari kuna haduwa ko da yaushe, domin ko abinci ne kake cin shi kullum to sai ya ishe ka, itama mace ai haka take.
•Yana da kyau kwarai ka zama gwani wajen furta kalaman so, suma suna taka muhimmiyar rawa, ka zama mai matukar tsafta, dan kuwa kamar yadda kake ganin ‘yan mata idan sun dau wanka ka ji sun birge ka, haka suma matan kalar wadannan samarin ke birge su.
A gaskiya sace zucciyar mace abu ne mai sauki ga wanda ya gane, sannan kuma abu ne mai wuya ga wanda bai gane ba. Tabbas idan dai har kana so ka yi wa mace satar zucciya, to dole ne sai ka bi dokoki kamar haka:
•Jan Aji: Ka sani fa mace ba za ta iya mallaka maka kanta hakan nan kawai ba, dole ne sai ta ja maka aji dan ta gane halayenka da hakurinka sannan kuma za ta so ta gane ko da gaske ne kake sonta ko ba da gaske ba ne. Saboda mata sun tsani duk wani saurayin da ke shirin yaudaransu, idan har ka ga ka zowa mace kai tsaye ta amince da kai ba tare da jan aji ba, to fa ka tsoraci lamarinta domin mace idan har cikakkiyar kuma gogaggiyar mace ce to za ta ja maka aji sosai har sai ka kusan yin kuka tukunna.
•Hakuri: Tabbas dole ne sai ka zama mai hakuri, idan ba haka ba to ba za ka samu damar lashe jarabawar da mace za ta yi maka ba, saboda za ka ga ababe da dama masu gasa zuciya, idan har ba ka zamo mai hakuri ba, to kai da yin soyayya da mace sai dai a hankali.
•Gaskiya: Mace tafi son saurayin da ke gaya mata gaskiya kai tsaye, idan har kai makaryaci ne to ina mai tabbatarma da cewa idan har ta zo ta gane sirrinka za ka sha kashi, domin haka ake kwatanta gaskiya dai-dai gwargwado.
– Kulawa: Dole ne idan dai har kana son zaman ka da mace ya dauki tsawon lokaci kuma ya sa ta soka sosai fiye da kima, to lallai kuwa dole ne sai ka kula da ita tamkar yanda za ka kula da kanka a lokacin da kake cikin rashin lafiya. Kulawa yana daya daga cikin siffofin abin da mata suke so.
– Rarrashi Tare Da Girmamawa: Mace tafi so idan har ka san ya ta yin fushi to ka rarrashe ta tamkar yanda za ka rarrashi jaririya. Kuma mace za ta ji dadi sosai fiye da kima idan dai har kana girmamata, ta fannin yabon halayen ta na kirki tare da nuna mata cewa babu wanda ka fi so a duniya tamkar ita saboda tana da halin kirki.
Akwai wasu halayyar da mace idan kana mata to ba za ta taba mantawa da kai ba. duk namijin mai wadannan halayya zai yi wuya mace ta manta da shi koda kuwa sun rabu. Wadannan halayya dai su ne kamar haka:

• Namiji wanda ya san kimar mace da kuma darajar ta.
• Namiji da yake yabon mace da ririta ta da daukar ta da mahimmanci.
• Namiji mai rikon amana wanda baya juya wa matarsa baya, komai tsawon shekarun da suka dauka da ko wacce larura ta gamu da ita.
• Namiji da yake bawa mace cikakken lokaci, domin sauraron ta da jin ra’ayin ta.
• Namiji mai kyauta.
• Namijin da yake bawa mace hakuri kuma ya lallashe ta idan ya bata mata rai ko kuma lokacin da ta shiga wata damuwa.
• Namiji da ya tsaratar da mace daga wani hadari da ta fuskanta a rayuwa.
• Namijin da mace tasan zai iya mutuwa saboda ita.
• Namiji mai fara’a da murmushi da sakin fuska da kuma tafiye-tafiye da mace.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button