Uncategorized

IZNAH PART 9 : Labari Cike Da Makirci

*9*
Cak ya tsaya tareda kallon rigarsa ahankali batareda yadamu da zafin da coffee din yakedashiba.
Mum asee ta qaraso da sauri cikin kulawa ta riqo rigar ta juyo cikin fa’da tace,
Anano meyasa Sam haryanxu qauyanci da hankali tareda nutsuwa sun kasa shiga cikin tosashen kanki?
Matsowa Kamal yayi ya riqo hannunta dake rawa sbd tsoro da fargaba ya kalli mum asee kafin ya maida kallonsa kan saheeb din yace,
Kayi hakuri natabbatarda batai da ganganciba tsautsayine.
A hannun Kamal din dake riqeda nata yafara sauke idanuwansa kafin ya dago ya Kalli fuskarta
Nan take kallonsa yasa jikinta ya qara daukar rawa Sai kawai tasamu kanta da saurin janye hannunta daga na Kamal din tanayin qasa da kanta.

‘dauke Kai yayi tareda juyawa yabar palon batareda yacewa kowannensu qalaba.
Da muguwar harara mum asee tabisa zuciyarta na qara quluwa cikin baqin ciki tace,
Gobe idan Zaki zuba Masa wani abu ki tabbatarda tafasasshe ne Kuma a zuciya ko fuska Zaki zuba Masa.
Cikin tsananin tsoro da mamaki ta ‘dago takalli mum asee din saitaga har cikin zuciyarta zancen yafito sbd tsananin tsana da qiyayyar data gani Yana tashi a fuskarta.
Tsaki tasaki tareda barin gurin yakurah nabin bayanta da sauri Kamal kuwa sake riqo hannunta yayi zaiyi magana ta zame tareda barin gurin da sauri sbd wani irin a jagule takejin zuciyarta.

Tana fama gyare gurin tafito da sauri zata koma tayi wanka daidai takusa Isa part dinsu Kamal daya biyota yayi saurin riqo hannunta tareda juyo da ita sauran ka’dan ta fa’da Masa daidai Nan shikuma ya canzo kayansa yafito idanuwanta suka sauka cikin nasa tayi saurin qwace jikinta daga Kamal tana ‘dauke Kai.
‘dauke Kai yayi shima tareda fadawa mota suka bar gidan a guje.
Kallonta Kamal yayi tareda ‘daure fuska sosai zaiyi magana Sai kawai ya fasa tareda juyawa zai bar gurin tai saurin Shan gabansa murya a karye tace,
Dan Allah karkayi fushi Dani.
Sake ‘daure fuska yayi tareda tureta gefe ya wuce Yana cewa,
Stupid village monkey.
Binsa da kallo tayi cikin sanyin jiki sbd taji abinda yace Amma zuciyarta takasa Jin zafin hakan saima haushin kanta dataji na 6atawa masoyinta Rai duk da dai ta lura yanxu yafara canza Mata sbd yanda yake yawan ta6ata dakuma tsawa dayake yawan yi Mata ga uwa uba zagi.

Juyawa tayi ta wuce tana shiga ‘daki a qofa taci karo da abdulshakur ya rarrafo Yana wasa.
‘daukarsa tayi cikin sanyin jiki ta qarasa ciki dashi sbd Inna na kicin tana aikin abincin ranan saheeb.
Zubewa tayi a katifa tareda ‘dora Abdul saman cikinta ta lumshe idanu Abu biyu na yawo akanta,
Maganar mum asee dakuma canxawar kamal.
Har gwaggo tagama tashigo tana kwance abdulshakur ma tuni bacci ya ‘daukesa ahaka.
Jin Kiran sallar la’asar yasa ta miqe tareda kwantarda Abdul ta tube tashige toilet tayo wanka tareda alwala.
Shiryawa tayi cikin doguwar Riga baqa tareda yafa gyalen rigar ta ‘dauko Abdul suka nufi qofar baya ta kicin din part din saheeb da gwaggo ke aikin yimasa abincin dare duk da kona ranar baidawoba bare yaci.

Kallon kicin din tayi sbd yafi nasu mum asee komai musamman ma kayan aikin.
Tuwon semon da gwaggo ke tuqawa ta kar6a tana cewa,
Gwaggo kawo nayi kije ki huta.
Kallonta gwaggo tayi tace,
Barmin aikina jeki kiji da naki ai…
Qarar fashewar Abu acikin palon ya katse zancen gwaggon a tare suka Kai kallonsu gurinda ta aje abdulshakur sukaga baya Nan Aida sauri tasakarwa gwaggo tuqin ta shiga palon.
Barbaza idanu tashiga yi tana neman inda yake sbd girman palon.
Zaro idanuwa tayi da qarfin Jin yasaki wata irin qara tareda kuka..
Da gudu ta qarasa gaban kayan kallon dake palon
Jini tagani ahannuwansa,
Frame din dake gurin ajiye da hoton nafeesa yajawo ya fasa kwalbar Kuma ta yankesa sosai.
Hoton takalla taji gabanta yayi mummunan fa’duwa ta ‘dauke kanta da sauri tareda duqawa ta ‘daukesa tana ‘dagowa Yana shigowa palon idanuwanta suka shiga cikin nasa saura qiris Abdul ya kubce Mata tayi saurin tarosa jikinta Sai rawa take sbd kukanda Abdul din yakeyi dakuma idanuwan da saheeb ya kafeta dasu.
Ahankali yakai kallonsa ga 6arnarda akai Masa yamaido kallonsa kan Abdul dake kuka sosai gashi takasa motsawa ya ‘dauke Kai tareda nufar hanyar stairs ya haye.

Kicin ta nufa da ‘dan sauri tahau wankewa Abdul hannuwansa Sai qara kuka yakeyi.
Daqyar tasamu jinin yafara tsayawa ta saka tissue data gani akicin din ta na’de Masa hannuwa tareda goyasa ta ‘dau tsintsiya da mopper takoma palon ta tattara gurin tareda cire hoton batareda tasake kallonsaba ta aje Kan receiver tafito.
Koda dare yayi wani zazzafan zazza6i yarufe Abdul Nan hankalinta yayi mummunan tashi sbd har wani irin zabura yake tayi kuka harta gode Allah,
Agogo takalla taga qarfe goma Sha biyu da minti ashirin miqawa gwaggo shi tayi cikin dashashiyar murya tace,
Bari naje nafadawa Kamal saimuje asibiti.
Hijabi ta ‘dora Kan doguwar rigarta ta barci ta fito ta nufi part din Kamal din dake facing na saheeb.
Knocking qofar tashiga yi ahankali.
Sake knocking tayi Amma still bai budeba saita qara qarfin knocking ‘din sbd yaji.
Motsi taji daga bayanta tai saurin juyawa cikin tsananin tsoro..
Ido hudu sukayi dashi ya bu’de qofar palonsa zai fito.
Saurin ‘dauke kanta tayi gabanta naci gaba da fa’duwa tanaji ya wuce ta ‘dan juyo tabisa da kallo yaje motarsa ‘daya ya bu’de ya ‘dauko wasu takardu yadawo.
Sauri sunkuyar dakai tayi ganin ya dawo daidainan Kamal ya bu’de qofarsa Yana ganin itace yayi saurin sa hannu ya jawota ciki idanuwanta suka sauka cikin na saheeb daya dawo kafin ta sauke idanuwanta Kamal ya tura qofar ya rufe.

Kallonsa tayi cikin tsananin damuwa hawaye na zuwa idanuwanta tace,
Abdulshakur ne ba lafiya sosai Dan Allah asibiti nakeson nakaisa ko chemist.
Kallonta yayi tareda zubewa Kan kujera Yana watsa Mata kallon banxa yace,
Dama sbd wannan ne Kika tadani bacci.?
Kallonsa tayi idanuwanta na kawo hawaye tace,
Dan Allah kayi hakuri bazan sake 6ata maka Raiba yanxu muje akaisa…
Qaramin kuka tasaki Dan dama Yana kusa.
Tsaki yaja da qarfi tareda miqewa ya wuce bedroom dinsa ya canzo Kaya yafito riqeda key din mota yazo yakama hannunta suka fito.
Kallonsa tayi cikin farin ciki da tsantsar sonsa tace,
Ngd.
Not to soon sbd idan Kika cigaba da rainamin hankali zakisha mamakina stupid village girl kawai.
Kallonsa tayi saima kawai taji yaqara shiga ranta taje da karbo Abdul da sauri tazo suka nufi wani babban pharmacy yasiya Masa magani suka dawo.
Koda gari ya waye lafiya qalau Abdul din yatashi ba wani zazza6i saidai kawai rashin qarfin jiki sosai.
Wanka tayi Masa tabasa abinci da magani kafin tabarwa gwaggo shi ta nufi gurin aikinta.
A hanya shiga Palo ta ha’du da Kamal wani lafiyayyan murmushi tasakar Masa ya ‘dauke gira daya Yana qare Mata kallo harsaidatazo daf dashi ya riqo qugunta Yana qoqarin hadata da jikinsa tayi saurin qwacewa takaici yasashi tureta da mugun qarfin tayi baya da qarfi Sai ajikinsa duk da haka hannunta Saida ya bugu da bangon gurin.
‘dago idanuwa tayi cike taf da hawaye suka ha’da Ido ta miqe ahankali tareda shigewa palon tana share hawayenta.
Fasa shiga palon yayi yajuyawarsa ya nufi mota yabar gidan.
Tsaki Kamal yaja tareda fiddo sigarinsa ya kunna yayi Mata mugun ja ya huro hayaqinta waje Yana cewa,
Stupid soldier man,,ka gama Jan ajinka da taqamarka hell is coming Cox nakusa kammala shirina akan tarwatsaka in and out you’ll be in worse than a hell for the rest of your miserable life,,,,
And for this stupi
d village idiot she and her bastard son sune zanyi amfani dasu na cimma burina and then fewwwww send them to heaven…
Dafasa yaji anyi da sauri ya juyo
Ajiyar zuciya yafara saukewa ganin mum asee tareda yakurah cikin Shirin zuwa gurin saheeb.
Sake Jan sigarinsa yayi tareda ‘dauke Kai yace,
The bastard just left ko minti biyar baiyiba so just keep all the pretendings aside mum asee and tell me ya muke ciki sbd haqurina fa yafara qarewa,
Zaman Nigeria Nan is fuckin killing me…kullum muna Abu daya akan samun dukiyarnan Amma mun kasa samu idan nace mu kashe monkey fool ‘din this stupid yeye girl din tace tanason ta auresa batason ya mutu yanxu and you mum is like all the evil ideas naki sun 6ace…
Gyara tsayuwa yakurah tayi cikin tsananin takaici itama sbd tanason saheeb Amma tafi son dukiyarsa dashi
mum asee ta ‘daukota riqo daga gidan marayu tun tanada qananun shekaru sbd kawai su cimma burinsu akan hakan Amma saheeb ya tsallaketa ya auri nafeesa sun kashe nafeesar Amma haryanxu ba wani biyan buqata itama dai Kam tafara Kai maqura.
Cikin baqin ciki tace,
Burina nacin dukiyarsa Yafi na banxar soyayyar danake Masa girma matuqar kirsa da emotional blackmail din mum asee baiyi Mana aikiba to Nima banga dalilin barinsa da raiba damacan nasone naji how good he is in bed….
Tsaki mum asee taja cikin tsananin takaici da baqin ciki
Ba qaramin Kai zuciyarta qarshe take ta danneba sbd mugun girman Kai da miskilancin saheeb,
Cikin qara takaici Kamal yace,
Believe it or not mum wannan bastard soldier step son ‘din naki ya daina sonki idan ba hakaba idan uwarsace shegen zai fitane baizo ya gaidataba hakama jiya wannan crazy carrot village girl din ta zuba Masa coffee ya wuce batareda yatsaya ko gaidaki yayiba hakama yau the psychopath ‘din fell on him and the gorilla decided to left without coming to see you again,
To ahaka shekara nawa kike tunanin zamu 6atar gurin jiran burinmu yacika.
Tabbas saheeb yanason ya canza sbd mutuwar nafeesat Amma Kuma wlh bazan yardaba,
Tun Ina budurwa nakeda burin mallakar wannan dukiyar ta Nan gidan Amma yayata damuke uwa ‘daya uba ‘daya tamin shigar sauri ta auri alhaji sbd ita ya nuna yanaso tun farko,,,
Tunda nake arayuwata bantaba son Abu na rasaba bazan iya kallo anty sakeena ta samu rayuwar da ni nake burin samuba shiyasa saheeb nada shekara biyar a duniya na zuba Mata madarar 6era a juice Ina zaune Ina kallonta tana roqona nakira alhaji ko iyayenmu Amma naqi ba kalar roqon dabataiminba Ina kallonta hartagama aman jinin ‘yayan hanjinta ta mutu nasamu daqyar na auri alhaji,
Yanxu saheeb yayi dukiyar datafi ta ubansa burina ya ninku matarsa taso kawon wargi nasa su bullet suka kaita dajin wani qauye suka cillata lahira tsohuwar Mai aikinmu tagano ainihin niyarmu yakurah ta taketa da mota ankaita asibiti acan muka biya Dr ya qarasa cillata lahira to duk wannan wahalar tanason tazama abanza wlh bazan yardaba dolene nasamu yanda nakeso Koda kuwa kowa nawa zai rasa ransa..
Kallonta Kamal yayi da manyan idanuwansa dasukai ja sbd 6acin Rai yace,
Yanda kikeji mum haka nakeji nama fiki Dan Nima Zan iya kawar da kowa akan hanyata when I said everybody I mean everyone…harma da Abba.
Kallonsa mum asee tayi cikin Dan takaici tace,
Dama kana tunanin idan Yana Raye zamu samu yanda mukeso ne?
Hmmm nayo Masa odar allura ta musamman dazata sa Yakoma gwara gawa dashi Dan idan muka kashesa saheeb yatafi ba sake waiwayarmu zaiyiba bare asamu biyan buqata shiyasa kawai Zan nakasashi Dan saheeb din ya dawo gaba daya ko yariga zuwa akai akai.
Murmushin Jin da’di yakurah tasaki sbd ganin komai zai tafiyar Mata ayanda takeso,
Bayan sun gama wahalar mallakar dukiyar zata aikasu indasuka iya aika mutane wato lahira.
Wani Abu Mai ‘dumi taji nabin qafafuwanta da sauri takalla taga fitsari ne ya kufce Mata sbd mugun abunda kunnuwanta suka jiye Mata su mum asee na fa’da.
Barin gurin tayi jikinta na tsananin rawa har qafafuwanta na hardewa sbd tsananin ki’dima da firgice..

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button