Uncategorized

Matar Aure Ta Kashe Budurwar Da Mijinta Zai Aura

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta kama wata matar aure da ake zargi da kashe budurwar da mijinta zai, kwanaki kadan kafin a daura auren.
Wadda aka kashe din mai suna Aisha, ta amince da auren Shahrehu Alhaji Ali, a kauyen Gimawa da ke Karamar Hukumar Doguwa ta Jihar Kano.
Abudllahi Haruna Kiyawa, wanda shi ne kakakin ‘yan sandan Kano, ya ce “A ranar 2 ga Janairun 2021, wani mutum Malam Kabiru Jafaru ya kawo rahoton bacewar ‘yarsa Aisha Ka, mai shekara 17 a ranar 1 ga Janairu, 2021.
“Daga bisani an tsinci gawar budurwar a wani kango, kuma da alamu an caka mata wuka a wuya ne.
“Daga nan aka dauki gawar aka kai ta Babban Asibitin garin Tudun Wada don ci gaba da bincike.
“Bayan gudanar da bincike ne jami’anmu suka kamo matar Shahrehu Alhaji Ali, wanda ake zargin ta da kashe budurwar saboda ta amince ta auri mijin nata,” cewar Kiyawa.
Ya kara da cewa yarinyar da aka kashe da mijin matar da ake zargi, sun shekara shida suna soyayya, har an sa ranar 9 ga Janairu 2021, a matsayin ranar da za a daura aurensu.
Ya ce bayan gudanar da bincike, wadda ake zargin ta amsa laifin da ake tuhumarta da aikatawa.
Ta amsa cewa ita ce ta kira Aisha zuwa wani kango, inda a nan ne ta soke ta da wuka a wuya, kirji da wasu sassan jikinta.
Kuma ta amsa cewa ta aikata hakan ne saboda kishi, don yarinyar na son ta kwace mata miji.
Kiyawa, ya ce an dauke wadda ake zargin zuwa sashen binciken manyan laifuka, don ci gaba da gudanar da bincike, kafin a tura ta kotu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button