Abun da yasa aure na ya mutu- Maryam Isah
Jaruma Maryam Isah wanda “half-sister” na Mansurah Isah ce tayi karin haske akan abunda ya janyo mutuwar auren ta na biyu wanda kwata kwata bai wuce shekara ba.
A wata tattaunawa da jaridar Blueprint jarumar tace ita kanta ba ta san hakikanin dalilin ba domin ba wani dalili ba ne mai gwari
“Malam abun da yake faruwa shine: maza sun dauka duk yar fim sauki gare ta, idan suka nemi kije gadon su, ki ka ki, sai su nemi ki da aure bayan kwanaki kadan sai su nemi dalili wanda bai taka kara ya karya ba su sake ki”
Jarumar ta bayyana rashin jin dadinta saboda a cewar ta kusan da kudinta aka yi auren amma mijin ya walakanta ta amma duk da faruwar hakan rayuwar ta bai kare ba.
“Yanxu haka ina aiki ne a foundation na yar uwa ta Mansurah Isah kuma ina fim; shekaru na 28 ne kacal kuma ina da kyau sannan abu kadan na rasa daga abubuwan da budurwa take da shi. A ikon Allah zan sake aure inyi rayuwar da ta fi da”