Uncategorized

Fadar shugaban kasa ta dauki harami, ana jiran dawowar Buhari

Fadar shugaban kasa ta dauki harami, ana jiran dawowar Buhari

Al’amura sun kankama a bangaren shugaban kasa dake fadar mulki ta Aso Rock, biyo bayan sa ran dawowar shugaban kasa Muhammad Buhari gida daga birnin London.

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya tafi birnin London a ranar 7 ga watan Mayu domin likitoci su cigaba da duba lafiyarsa.

Matar shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari, wacce ta dawo kasarnan ranar Talata, tace mijinta zai dawo gida nan ba dadewa ba.
cewa ta kuma ce mijin nata yana warkewa cikin sauri.

An rawaito tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, na cewa shugaban kasa Buhari dai dawo gida kafin ranar 11 ga watan Yunin da muke ciki.

Duk da cewa babu wata sanarwa da aka fitar kan dawowar shugaban, an samu canje – canje da dama fadar shugaban kasa wanda alamune dake nuni da shugaban ya kusa dawowa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button