Uncategorized
Muhimmancin Kiss Ga Ma’aurata: Kwararan abubuwa 6 da sumbata ke yi wajen inganta lafiyar mata da miji
Advertisment
BI MOHAMMED LERE:
A wani rahoton musamman da CNN ta wallafa a a shafinta na yanar gizo, wasu kwararriyar likita ta ambato wasu kwararan abubuwa 6 da sumbata ke yi ga lafiyar musamman mata da miji.
Dalla-Dalla a nan:
1 – Sumbata na dauke matsanancin ciwon kai da kuma azabar ciwon mara a lokacin da mace ke al’ada.
Bayanan nazarin ya nuna cewa a lokacin da kanka ko kanki ya ke dan karan ciwo, mai makon ka kaurace wa matarka ko mijinki, jawo hannun sa ki sumbace shi mai tsawo, zaki ji kamar kin sha Fanadol ne.
2 – Sumbata na kau da cutar lalacewar hakura da dasashi. Saboda yawan miyau da dukkan ku kuke fitarwa a lokacin, yakan garwayu ya kashe wasu cututtukan dake sa a samu matsala irin haka.
3 – Sumbata na rage hauhawan jini. Masana sun ce idan aka dade ana sumbata, yakan daidata bugawar zuciyar mutum sannan ya daidaita malalar jini a jiki ta yadda komai zai gudana ba tare da ana samun matsala ba.
4 – Sumbata na sa ka samu lafiya a jikin ka. Idan baka jin dadi, ko kuma kana jin gajiya da damuwa, garzaya ga matar ka ko mijin ki. Da an gana za a samu nishadi nan take.
5 – Yawan Sumbatar matar ka ko mijinki na kona sinadarin Kaloris dake sa kiba a jiki. Idan aka dage za samu raguwar ki ba.
6 – Sumbata na gyara kyawun fuska da tsayuwar sa.
Dr Per Demirjian, ta shaida cewa idan aka dade ana sumbata na tsawon lokaci akai akai, akwana a tashi za aga fuska yana kyau yana daukar saiti.
CNN ta ce ta samo wannan rahoto a shafin upwave.com.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com