Uncategorized
HAILA TA SAME NI BAYAN MIJINA YA SADU DA NI ?|DR JAMILU YUSUF ZAREWA
Advertisment
HAILA TA SAME NI BAYAN MIJINA YA SADU DA NI ?
Tambaya:
Assalamu alaykum, Malam ina da tambaya,mace ce bayan mijinta ya sadu da ita, kafin ta yi wanka Sai jini ya xo mata ya xa ta yi wanka, shin gabadai xatayi niyya ko kuma wannan na biyun xa tayi?
Amsa:
Wa alaikum assalam, za ta jira in ta samu tsarkin haila sai ta yi wanka daya kawai.
Yana daga cikin ka’idojin SHARIA Idan ibadoji guda biyu suka hadu, kuma manufarsu ta zama guda daya, sannan za’a iya hada su a lokaci guda, to sai daya ta shiga cikin dayar.
Yana daga cikin ka’idojin SHARIA Idan ibadoji guda biyu suka hadu, kuma manufarsu ta zama guda daya, sannan za’a iya hada su a lokaci guda, to sai daya ta shiga cikin dayar.
Wannan yasa mai janabar da jinin haila ya same ta kafin ta yi wanka, za ta wadatu da WANKAN karshe, saboda saukin musulunci da kuma daukewa jama’a abin da zai kuntata musu, kamar yadda aya ta karshe a suratul Hajj ta tabbatar da hakan.
Allah ne mafi Sani.
Allah ne mafi Sani.
Amsawa: Dr Jamilu Zarewa.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com