Uncategorized

Wasu Mutane Da Ba’a San Ko Su Waye Ba Sun Kone Wani Mutum A Garin Kura Dake Jihar Kano

Wasu Mutane Da Ba’a San Ko Su Waye Ba Sun Kone Wani Mutum A Garin Kura Dake Jihar Kano

A ranar Larabar da ta gabata ne da tsakar dare wasu da ba’asan ko su wane ba suka je karamar hukumar Kura dake jihar Kano da wannan bawan Allah a cikin mota a daure, daidai titin zuwa kauyen Bugau bayan Nitel suka tsaya suka fito dashi suka kone shi kurmus sukayi tafiyarsu.

Fulanin dake kusa da wajen sun shaida hakan, domin sune suka ankarar da abin dake faruwa, kafin ayi yunkurin daukar mataki har sun kone shi sun gudu.

Wayewar gari jami’an tsoro sunje sun tafi da gawar zuwa babban sashin bincike na hukumar ‘Yan Sanda ta jiha. Sai dai ana kyauta zaton mutanen daga cikin birnin Kano suka fito da mutumin.

Allah ya tsaremu, ya tsare mana imaninmu.

Daga Shafin Hausa Daily

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button