Dalilin Da Ya Sa Farashin Hajjin Bana Ya Yi Tsada – Hukumar Hajji
Hukumar Hajji ta kasa ta bayyana dalilan da suka sa farashin zuwa hajji a bana ya karu da kaso 50 cikin dari.
A bana dai maniyyata a kowacce jaha a Nijeriya za su biya sama da miliyan daya da dubu dari biyar domin sauke faralin, sabanin Naira 998,248.92 na karamar kujera, da Naira 1,047,498.92 na matsakaiciyar kujera, da kuma Naira 1,145,998.92 na babbar kujera da maniyyata daga Arewacin Nijeriya suka biya a bara.
A wannan shekarar, farashin bai daya maniyyatan za su biya, dai dai da yadda kowacce jaha ta kayyade. Mafi karancin farshin shine miliyan daya da dubu dari biyar.
Hukumar hajjin ta ce an samu wannan kari ne a sakamon faduwar darajar Naira, duk kuwa da rangwamen farashin dala da gwamnati ta yi wa mahajjatan.
A wata hira da kafar yada labarai na BBC ta yi da shugaban hukumar, Alhaji Abdullahi Mukhtar Muhammad, ya bayyana cewa karin ya tsaya a kaso 50 ne saboda wannan rangwame.
Wannan lamari dai ya sanya maniyyata da dama fasa sauke faralin a bana.