Uncategorized
FATAWAR RABON GADO (78)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA
*FATAWAR RABON GADO (78)*
*Tambaya*
Assalamu alaykum
qanina ne ya rasu ya bar mata daya da yaransa mata guda uku da mahaifinsa
Shi ne nace ya gadonsu zai kasance ?
qanina ne ya rasu ya bar mata daya da yaransa mata guda uku da mahaifinsa
Shi ne nace ya gadonsu zai kasance ?
*Amsa*
Wa alaikum assalam, Za’a raba abin da ya bari gida:24, a bawa matarsa kashi:3, sai a bawa ‘ya’yansa mata kashi:16, ragowar kashi biyar din sai a bawa mahaifinsa. Kashi hudu a matsayin (sudus) dinsa, kashi dayan kuma saboda shi ne Asibi.
Allah nemafi sani
19/11/2016
*Amsawa*
*DR Jamilu Zarewa*
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com