Innah lillahi wa’innah Alaihi raju’un:Allah yayiwa Sheikh muhammad Rabiu Daura Rasuwa
Innah lillahi wa’innah Alaihi raju’un
ALLAH yayiwa babban mallamin nan kuma jigo na kungiyar izalatuh bidi’ah wa’ikamatus sunnah Allah yayi wa sheikh muhammad Rabi’u Daura Ratsuwa a yau.
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!
Shugaban Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau yana gayyatar ‘yan uwa musulmi zuwa wajen jana’izar Daya daga Cikin dattawan wannan kungiya da ya rasu a yammacin juma’ar nan Marigayi Sheikh Muhammad Rabi’u Daura
Za’a gabatar da Jana’izar ne a Masallacin Danfodio Dake unguwar sunusi a garin kaduna da misalin karfe tara na safe in Allah ya kaimu.
Sheikh Abdullahi Bala Lau, Sheikh Kabiru Gombe, Sheikh Abdulbasir Isah U/maikawo tare da sauran manyan Malamai tuni sun isa birnin na Kaduna a shirye shiryen fara jana’izar Malam.
Allah ya gafarta masa ya saka Ladan aikin da ya yiwa addini a mizani. Amin.