Uncategorized
Buhari zai tura sojoji da jiragen Yaki Gambiya Don kifar da jammeh
Buhari zai tura sojoji da jiragen Yaki Gambiya Don kifar da jammeh
shugaba muhammad Buhari ya tanadi sojoji 800 da jiragen yaki wadanda za su kasance cikin shirin ko ta kwanan don hambarar da shubagan Gambiya mai barin gado ,yahya jammeh idan ya ki mika mulki ga zababben shugaban kasar Adam barrow
Rahotanni sun nuna cewa an umurci rundunar wadda aka yi wa lakabi da ECOMOG NIBATT 1 da ta kasance a makarantar hotas da sojoji da ke jaji a jahar kaduna.
shugaba jammeh ai ya yi alwashin ba zai mika mulki ba a ranar 19 ga wannan wata ba har sai kotun koli ta yanke hukunci kan karar da ya shigar na kalubalantar sakamakon zaben wanda kuma hakan zai faru ne a cikin watan mayu.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com