Ba abin da zai hana ni zama shugaban Gambia – Barrow
wanda ya lashe zaben shugaban kasar Gambia Adam Barrow yace ko ana ha mza ha mata sai ya sha rantuswar kama aiki a zaman shugaban kasar Gambia a makon gobe.
A cikin wata hira da BBC mr.Barrow yayi kira ga shugaba mai ci yanzu yahaya jammeh da ya zo su tattauna ido da ido domin warware rikicin siyasar kasarsu gabacin wanannan ranar 19 ga wata janairu.
kalaman nasan na zuwa ne sa’oi gabanin isar tawagar masu shiga tsakanin tsakanin kungiyar ECOWAS zuwa kasar domin ciwo kan yahaya jameh ya sauka a cikin lumana
“wa’adin mulkinsa zai kare 12 na darenna ranar 18 ga wata,don haka a hukumance zan kasance shugaban kasar a 18 ga watan janairu,kuma ko ana ha maza ha mata sai an rantsar da ni in Barrow”